-Advertisement-
-Advertisement-
Facebook ta sanar da kaddamar da wani sabon manhaja da zai tamaki masu anfani da kafar ta Facebook wajen kulla alaka da mutanen da zasu iya ci gaba da soyayya tare.

Mai kanfanin na Facebook, Mark Zuckerberg ya bayyana haka a babban taron kanfanin mai taken “Facebook’s F8 Conference” da aka gudanar a garin San Jose, California ta kasar Amurka.
“In muna hankoron taimakawa mutane wajen karfafa dandantaka tsakanin al’umma to wannan sabo shirin shi ne zai fi bayar da ma’ana fiye da sauran, saboda haka a halin yanzu zamu kaddamar da shiri na musamman mai dauke da sabbin abubuwan da zasu taimaka wajen kulla alaka tsakanin samari da ‘yanmata” inji shi
Zuckerberg ya kara karfafa cewa, wannan sabon tsarin nada nufin samar da dangantaka mai dorewa ba wai na wucin gadi ba.
Ya ce, “A kwai mutum fiye Miliyan 200 a farfajiyar Facebook da suka alamta cewa, basu da mata ko basu mazaje, lallai ya kamata ayi wani abu a kan haka”
Sabon manhajar ba zai bar abokai a Facebook su iya ganin bayanan abokansu ba, wannan na a matsayin sharadin tabbatar da sirri a tsarin tafiyar da manhajar.