-Advertisement-
-Advertisement-
A ranar Talata ne, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir el-Rufai, ya yi barazanar kashe duk wani bakon da ya shigo kasar nan domin ya tsalma bakinsa a kan babban zaben kasar nan.

Ya yi wannan barazanar ne bayan mako guda da Gwamnatin tarayya ta zargi wasu manyan kasashen Duniya da suka hada da kasashen Amurka, Ingila da tarayyar Turai, da aikata wani abin da zai iya zama katsalandan a cikin harkokin da suka shafi kasar nan, sai ya yi gargadi a kan hakan.
Zaben Shugaban kasa wanda za a fara da shi a ranar 16 ga wannan watan na Fabrairu, ana sa ran zai zama mai zafin gaske ne a tsakanin ‘yan takaran, ana ma tsoron barkewar rikici da kuma aikata magudin zabe a cikin sa, a inda Jam’iyyun adawa suke ta nanata zargin da suke yi wa Jam’iyyar da ke kan mulki na tana shirya makarkashiyar yin magudi a zaben.
Sau da yawa, Shugaba Buhari, ya sha yin alkawarin gudanar da zaben a bisa gaskiya da adalci, yana kuma yin gargadi ga kasashen waje da su kasance ‘yan baruwanmu a kan harkokin da suka shafi cikin kasar nan.

A makon da ya gabata ne, Ministan harkokin waje na kasar nan ya ce, sun lura kasashen Yammacin Turai, suna nuna alamun son kai ga Jam’iyyar PDP, abin da ya kira da ya sabawa ka’idojin zamantakewa na Duniya.

El-Rufai, wanda dan Jam’iyyar APC ne, ya tsananta kai hari ga Jam’iyyun adawa da kuma kasashen Duniya a tashar Talabijin ta kasa a ranar Talata, inda ya bayyana a wani shiri na Tashar ta NTA, wanda, Cyril Stober, ke gabatarwa kai tsaye.

“Duk masu kiran wasu da su zo su tsalma mana baki a nan Nijeriya, muna nan muna jiran duk wanda zai zo ya tsalma mana bakin na shi, za kuwa su koma a matsayin gawa a cikin jakunkuna,” in ji Gwamnan.
Ya kara da cewa, a lokacin da Nijeriya ta tsalma bakinta a kasashen Sierra Leone da Laberiya a shekarun 1990, ta yi hakan ne a bisa shawarar da al’ummun Duniya suka bayar, a matsayinmu na makwabtan su.
El-Rufai ya ce, Nijeriya kasa ce mai ‘yancin kanta, wacce ba za ta taba yarda wata kasa daga waje ta nemi keta mata ‘yancin da take da shi ba.

Wannan gargadin na El-Rufai, tamkar karfafa gargadin da wani Kakakin Shugaban kasa, Garba Shehu ne ya yi a watan da ya gabata, inda yake cewa, Nijeriya ba za ta yi wata-wata ba wajen aikewa da dakarunta a kan duk wata wata kasar wajen da ta nemi yi mana katsalandan a cikin harkokin cikin kasarmu.

Sai dai Garba Shehun ya fito yana nuna jin dadinsa da abin da wasu Gwamnonin Jihohi guda biyu na Jamhuriyan kasar Nijar suka yi, inda suka tako har cikin kasar nan da sunan sun zo ne su taya Shugaba Buhari yakin neman zabe a ranar 31 ga watan Janairu, lokacin da Shugaba Buhari, ya je kamfen din neman a sake zaban na shi a Kano.

Ministan yada labarai, Lai Mohammed, wanda ya jima yana yin gargadi a kan yin kalaman batunci, bai maido da amsa a kan bukatar da aka yi ma shi ba na ya ce wani abu a kan maganan da dan Jam’iyyar na su ta APC ya yi. Hakanan shi ma Kakakin Jam’iyyar ta APC, Rundunar Sojin Nijeriya, Ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya, duk sun ki cewa uffan a ranar Laraba da safe a kan maganan da dan’uwan na su ya fada.