-Advertisement-

-Advertisement-
Wata kotun birnin Madrid ta kasar Sipaniya ta yanke wa gwarzon dan kwallon Juventus, Cristiano Ronaldo hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari bayan ta same shi da laifin kauce wa biyan haraji.

An kulle Ronaldo a kotu

Koda yake kotun ta yi masa sasssauci, in da a yanzu ta dora masa biyan tarar Euro miliyan 18.8, tarar da tuni Ronaldo ya amice da ita batare da bata lokaci ba domin gujewa zaman gidan yari.

Ronaldo ya isa harabar kotun ne a ranar Talata bayan kotun taki amincewa da bukatarsa ta farko ta bayyana a faifen bidiyo domin yi masa shari’a saboda bashi da lokadin halartar kotun tun farko. An zargi dan wasan ne da kin biyan haraji tsakanin shekarun 2010 zuwa 2014, lokacin da yake kan ganiyar buga wasansa a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid inda yashafe shekaru tara yana buga kwallo.

Ronaldo mai shekaru 33 na cikin attajiran ‘yan wasa a duniya, in da mujallar Forbes ta bayyana shi a matsayin na uku a jerin ‘yan wasan da suka fi arziki a duniya kuma na biyu a nahiyar turai. Ronaldo wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau biyar a Turai, ya samu rakiyar budurwarsa, Georgina Rodriquez da dansa guda daya sannan kuma tuni ya koma birnin Turin na kasar Italiya domin cigaba da daukar horo.