-Advertisement-
-Advertisement-
Itadai in-ina cutace wacce take hana mutum furta wasu lafuzza ayayin da yake magana,
Ko kuma ta haifarwa mutum da jinkiri wajan furta wasu lafuzza.
Maganin Cutar In'ina, cutar inina
Maganin Cutar In'ina
Akwai wanda saboda tsananin in-ina harsai ya zubda hawaye kafin ya iya furta magana ko lafazi.

IN-INA TA KASU GIDA BIYU.
1- akwai wadda ake haihuwar mutum da ita (wacce mutum ya gada kenan).
2- akwai kuma wadda mutum yake kamuwa da ita rana tsaka tun yana dan karami ko kuma bayan girman sa.

NAU'IN IN-INAR DA AKE WARKEWA:
In-inar data samu mutum rana tsaka tun kuruciya ko kuma bayan girman mutum itace muke magana akanta.

MAGANINTA
Asamo Zuma mai kyau Ingantacciya, ''Yar gida ba yar waje ba, sai a nemi gishiri a cakuda zumar da gishirin ta inda dandanon gishirin zai bayanna acikin zumar, amma ba mai kama baki ba. (ma'ana kar gishirin yayi yawa)

YADDA ZA'A SHA.
Za'a dinga sha sau Biyu a rana, kafin aci abincin safe da kuma lokacin kwanciya bacci da daddare.

NOTE : Ba lokaci guda ake warkewa ba a'a, sai anjure amfani da maganin a hankali waraka zata samu, Da yardar Allah.

Wannan maganin mutane dayawa sun gwada kuma An dace.
Allah yasa adace Amin.
idan ka karanta kayi sharing don wasu suma su amfana, kaima kasamu Ladan.