-Advertisement-
-Advertisement-
Hukumar 'yan sanda masu binciken manyan laifuka da ta'addanci na Kasar Amurka wato Federal Bureau of Investigation (FBI) ta bayyana wasu mutane biyar masu matukar hatsari a duniya wanda take nemansu ruwa a jallo, da kuma bayar da kyauta mai tsoka ga duk wanda ya taimaka aka kama daya daga cikinsu.

mutane 5 da duniya take nema ruwa a jallo


1- Mutum na farko: sunansa Major General Qassem Suleimani shugaban rundinar tsaro na Kasar Iran Laifin da ya aikata: Shine yake jagorantar yakin da kawancen sojojin Iran sukeyi da dakarun Amurka da Isra'ila, yana daukar nauyin 'yan ta'addan da suke kaddamar da harin ta'addanci musamman a Kasar Syria inda dubbannin mutane suka hallaka, kuma ya taimaka wajen tabbatar da shugaban Kasar Syria akan shugabanci.

An bayyana cewa wannan babban hafshin soji na Iran yana da kusanci sosai da jagoran gwamnatin juyin juya hali na Kasar Iran.

2- Mutum na biyu: Sunansa Ibrahim al-Asiri wanda yafi shahara da sunan Abu Saleh, kwararre ne a bangaren kera bama-bamai masu linzami wa Kungiyar al-Qaida a Kasar Yemen, tsohon dalibin Chemistry ne wanda yake da baiwa na sanin sinadarai da yadda a ke hada kayan fashewa, kamar yadda jami'an tsaron sirri (Intelligence) suka bayyana, sunce shine wanda yake horar da 'yan kungiyar al-Qaida yadda ake kera kayan fashewa.

A shekarar 2014 kayan leken asiri na Kasar Amurka sun gano shi a wani tsibiri dake kudancin Kasar Yemen, anso ayi amfani da jiragen yaki marassa matuki a hallakashi to amma sai akayi la'akari da wadanda harin jiragen zai rutsa da su.

3- Mutum na uku: Abubakar Shekau shugaban kungiyar Boko Haram a Nigeria, babu dogon bayani a kan waye Abubakar Shekau da kuma illa da ta'adinsa a Nigeria domin sananne ne a gurin dukkan 'yan Nigeria.

4- Mutum na hudu: Sunansa Sun Kailiang 'dan Kasar China ne, kwararre ne a harkan kutse wa na'ura mai kwakwalwa (Super hacker), sojan Kasar China ne yana da mukamin Kyaftin.

Laifinsa da ake tuhumarsa dasu shine yana kokarin rusa tattalin arzikin Amurka ta hanyar yiwa manyan na'urorin Kasar kutse wanda suke kunshe da bayanan sirrin tsaron kasuwancin Amurka, da kuma makamin ta na Nukiliya ta yadda idan ya samu nasaran yiwa na'urorin da suke lura da Makamin Nukiliyar zai ita tada makamin.

A dalilinsa ne Amurka ta kirkiri wata cuta (virus) amma wacce zata iya illata na'ura ta yanda zata iya lalata duk wata na'ura da take kokarin yin kutse, sannan ta saka mata cutar da zata lalata na'urar, tun kafin na'urar mai kutse ta dauki hoto da kwafin hanyar shiga (password) na na'urar da akeso a yiwa kutse.

5- Mutum na biyar: Sunansa Mokhtar Belmokhtar 'dan Kasar Algeria ne, kuma shine shugaban tsagin Kungiyar al-Qaida a yammacin afirka (Maghreb).
Shine yake tsara ayyukan ta'addanci na kungiyar al-Qaida, yana daukar nauyin matasa da ake kawosu daga sassan duniya ana kaisu Algeria suna koyon ayyukan ta'addanci a gurinsa.

A takaice wannan shine bayanin mutane biyar masu hatsari wanda hukumar FBI take nema ruwa a jallo, akwai kyauta mai tsoka ga duk wanda ya taimaka aka kama daya daga cikinsu, wanda yake da bayanan sirri a kansu ya jarraba Allah Ya sa a dace.

Rubutawa : Datti-Assalafy