-Advertisement-

-Advertisement-
" kin wani tsaya min akai, idan za ki iya zama sai ki samawa kanki wurin zama idan bazaki iya ba ga hanya don bazan lamunci a tsaya min aka ba"
Duk wannan maganar da ya ke yi, bai cire idonshi da ga kan laptop d'in da ke gabanshi ba.
sakaci hausa novel,  hausa novels

Ta rasa mai yasa har yanzu ta kasa sabawa da irin bak'ak'en maganganun da ya ke yawan ya6a ma ta.

Cikin sanyin jiki ta samu kujera gami da zama, ta cigaba da bin office d'in da kallo tabbas Dr Umar mutum ne mai tsafta ga aji.
Sanyin A.C ne ya cigaba da ratsata had'e da wannan k'amshin da ke tare dashi ako da yaushe, k'amshin da ya ke sawa ta shiga wani irin yanayi aduk lokacin da ta shak'e shi.

Ita kam bata ta6a jin irin wannan k'amshin a jikin kowa ba sai Dr, wannan yasa ta dad'a yarda k'amshin na shi na daban ne, kamar yadda ma'abocin k'amshin ya kasance.

Tabbas da zata san turaren da ya ke anfani da shi da ta siyawa Ahmad d'inta a matsayi gift, wani irin yanayi ta fara shiga lokacin da ta tuno da abin k'aunarta.
"Allah sarki my man da kana gari da kai zan fara nema"
A cikin zuciyarta ta yi maganar ba ta san ya fito fili ba, sai jin tsakinsa ta yi, kafin kuma ya k'ara da cewa.

"Kunya cikon imani ce, tur da macen da ta d'auki soyayyar d'a namiji, abu mai mahimmanci a rayuwarta, wannan rashin zuciyar har ina, mutun kamar wanda kare ya cinyewa zuciya, haba! "
Yana gama fad'an haka ya fice da ga office d'in.

Wani irin bak'in ciki ne ya ziyarce ta to wai mai Dr Umar ya ke nufi da ita ne, shekara talatin da biyar, shin zata yita zama haka ne ko kuma so ya ke ta k'are rayuwarta cikin bak'in ciki, tabbas da wani ne daban, ba Dr ba da sai yayi danasanin saninta rayuwarshi, tabbas Dr yaci darajar masu daraja.

Sanin halinshi zai iya tafiya ya barta yasa ta tashi don binshi tunda bata da za6i.
Gaban motar ta bud'e ta shiga kusa da kujerar driver ta zauna kafin ta rufe kofar, tayar da motar yayi cikin nutsuwa ya fara tuk'awa wayarshi ce ta fara ruri alamar ta na neman agaji.

D'auka yayi gami da yin sallama can ta ji ya ce "ga tanan muna ma haryar gidan"
Wannan ne ya tabbatar mata da Babanta ya ke wayar, yanzu haka yayita nemanta a waya bai samu ba, tunda ta fito daga tiyata ta manta bata kunna ba.
Tafiyar kurame suka yi, ba wanda ya ce da d'an uwansa komai har suka iso kofar gida kafin ya k'arasa tsayawa ta bud'e murfin motar ta fita, ta na jinshi har sai da ta shiga kafin yaja motarshi, ta san yaji haushin hakan da ta yi.

Shigarta falon ta tarar da su Baba basuyi bacci ba suna zaman jiranta, Allah sarki iyayena ta fad'a a zuciyarta.
kafin kuma taje garesu had'e da yi musu sannu da gida suka ansa had'e da tambayarta dalilin jimawarta tunda ba ta ta6a kaiwa wannan lokacin a waje ba, sannan ga wayarta a kashe.

Aunty ta ce "Farida hankalinmu ya tashi ga Alhaji nan ko abinci bai ci ba bare kuma ya kwanta, ga wayoyinki duk a kashe"
"Ku gafarce ni iyayena motata ce tak'i tashi, wayoyina kuwa tunda na fito daga tiyata na manta ban kunna ba" Farida ta fad'a cikin ladabi.

Cikin damuwa Baba ya ce 'gaskiya ya kamata ki canja mota Farida, domin na fuskanci motar ta sa ki agaba"
"Toh haka nake so Baba, amma kuma akwai abubuwa a gabana inaga sai zuwa bayan bikin nan"
Wannan karon Aunty ce ta yi magana
"Toh amma haka za ki yita fama kullum ta na tsaya miki a hanya Farida"
"Ba komai Aunty zan lalla6a ta har zuwa lokacin da zan sauya, yanzu dai kuje ku kwanta nima nagaji zan je na kwanta"
Baba ya ce "toh Allah ya shige mana gaba, amma dai zakici abincin kafin ki kwanta ko?" murmushi ta yi had'e da cewa.
"Babana kenan, ai ba zan zauna har wannan lokacin banci komai ba, ai aikin ma baze yuwu ba"
Ta fad'a ne kawai don ta kwantar musu da hankali amma rabonta da abinci tun wanda sukaci tare da su Maryam kuma a yanzun ma ba ta jin zata iya saka wani abu a cikinta.

------Arewas" kin wani tsaya min akai, idan za ki iya zama sai ki samawa kanki wurin zama idan bazaki iya ba ga hanya don bazan lamunci a tsaya min aka ba"

****
Jakar hannunta ta ajiye gami da rage kayan jikinta don tana bukatar ta gasa jikinta, wayarta ta kunna.
Ta na kunnawa kiranshi ya shigo, murmushi ta yi, ta san ya jima ya na nemanta, ga shi tun safe rabonsu da yin waya, yanzun ma dai bazata d'aga ba har sai ta fito da ga wanka.
Tawul ta d'aura gami da cewa "afwan my man sai na fito zan d'aga wayar".
Ba yadda ta so ba, haka ta fito ba tare da ta gasa jikinta ba, domin ya kasa hakuri da kiran, ita kuma ba zata iya juran rashin d'aga wayarshi ba, ko goge jikinta batayi ba ta d'auko wayar amma kafin ta kai ga danna ma6allin ansa waya, wayar ta katse.
Ganin yawan misscall d'in da ta gani nashi yasa ta zare ido don tasan ta mai laifi, kafin takai ga kira har wani kiran nashi ya shigo, wannan karan cikin sauri ta d'aga wayar kafin kuma ta kara a kunnenta, muryarshi taji yana cewa.
"Dear lafiya yau ina kika shiga hankalina ya tashi matuk'a, kuma inata kiran wayoyinki amma duk a kashe, yanzu kuma na yi ta kira baki d'aga ba"
Cikin muryarta mai dad'in sauraro ta ce " my man kayi hakuri wallahi mantawa na yi da na fito daga tiyata ban kunna ba, sannan naga kiranka daf da zanshiga wanka ban d'auka ba na ce "saina fito"
"Anya Dear kindamu dani kamar yadda kike yawan fad'a kuwa, gani nan nakasa samun sukuni yadda kika san na zama tsuntsu nazo na ga lafiyarki nake ji na ka sa ta6uka komai amma ke naga abun bai ma dameki ba" ya fad'a cikin damuwa.
"Haba my man ina tunanin kafi kowa sanin yadda nake sonka kuma na damu da Kai nasan kuma zaka bada sheda akan haka, kayi hakuri ina neman afwa abisa laifina" murmushi yayi har sai da ya ratsa kunnunwata, sannan ya ce.
"ba komai Dear ai bakya laifi awurina sam ba na iya yin fushi da ke".
Allah kad'ai yasan irin farin cikin da ta ke shiga aduk lokacin da ta ke ta re da Ahmad ko da kuwa a waya ne, tabbas ta yi sa'an masoyi na gaskiya.
Cikin murya mai cike da shauk'i ta ce " wallahi My man halayenka masu kyau sune su ke k'aramin k'aunarka, My man na sallama maka zuciyata"
"Kai don Allah Dear fad'a min yadda kike ji a zuciyarki dangane dani ko zan samu nutsuwa" Ahmad ya fad'a cikin tsananin farin ciki.
"Ba zan iya kwatanta maka ba my man amma nasan kai ne sanyin zuciyata, My man wani lokaci ina jin nafi kowace mace sa'an samun gwarzon masoyi"
Wannan kalaman na ta sunyi matuk'ar sanyaya mai rai, har sai da ta gane hakan a muryarsa, cikin tsananin k'auna ya ce.
"Dear ni kad'ai nasan halin da nake ciki, ni kad'ai nasan irin yadda nake jinki a raina, bazan iya jure rashinki a rayuwa ba"
Wani irin ajiyar zuciya yayi har sai da ta gane hakan, sannan ya cigaba da cewa.
"Dear na rok'eki karki gujeni duk rintsi ni kuwa na miki alk'awarin zan zame miki mijin marainiya, mijin da ko wace mace ta ke fatan samu, abin k'aunata! bani da burin da ya wuce kizama mallakina, har gani na ke lokaci baya tafiya, maganar gaskiya idan na rasaki zan iya mutuwa Dear, ba zan iya rayuwa ba ta re da ke ba"
"My Man ta ya-ya zan guje ka, kai baka gujeni ba sai ni? Karfa ka manta ni d'in fa mai rauni ce amma ka dage kai da fata sai ni, na riga na sa ni idan na rasa ka ba zan ta6a samun kamar ka ba, har na gama sauran rayuwata, tabbas idan na rantse akan hakan ba zanyi kaffara ba"
"Shishshshsh" ya katseta, sannan ya d'ora da fad'i " Faridaaa kinga wurin da raina zai 6aci kenan, ba tun yau na ke fad'a miki ba, ba nason kalmar raunin nan da kike yawan anbata wa kanki, wallahi banaso shin ba za ki daina ba"
Wani irin yanayi ta shiga har sai da taji hawayen da ta ke mak'alewa yana shirin zubowa, cikin shaukin so ta ce.
" Na daina bazan sa ke ba na daina, ba na so ranka ya 6aci amma nima ka daina ambaton zan rabu da kai, My man mutuwa ce kawai zata rabamu"
Murmushi yayi sannan ya ce " nifa ko mutuwar ce ina rok'o Allah akan ta fara d'auke ni domin Allah yasani bazan iya juran rashinki ba"
Itama murmushin ta yi sannan ta ce " kaji son kai, to saidai fa mu mutu tare, nikam My Man mubar wannan maganar mu koma wa ta"
Ya ce " toh matata an daina, amma fa ya kamata kije ki kwanta haka nasan kingaji da yawa, ki samu ki huta ba dan nagaji da jin muryarki ba" cikin sassanyar muryarta ta ce
"toh My Man kayi mafarki na"
Ya ce "ai kinsan wannan dole ne, ki kulamin da kanki please karfa ki manta kiyi addu'a kafin ki kwanta, I love you so much "
Ta ce "angama mijina and I love you more"
kowannensu ya kwanta cikin kewar d'an uwanshi, had'e da mafarkai kala-kala.
*******
Falon ya d'auki shuru badda k'aran AC da fanka da suke aiki bakajin komi, Farida ce ta katse shurun da cewa.
"please karkusa na k'ware mana duk kunsa min ido" Jidda ce ta ce.
"toh gani mukayi kintsaya cin yanga bayan kinsan ke muke jira" Ita kuwa Maryam murmushi ta yi.
Alokaci guda fara'an kan fuskarta ya juye zuwa damuwa, dubansu ta yi, sannan tace
"Yau zan baku tarihin rayuwata wanda na ke so yazama izna ga y'an baya"
Hawaye ne ya zubo kan kuncinta sannan ta cigaba da cewa "a zahirin gaskiya kune mutane na biyu da ni da kaina na ta6a basu tarihin rayuwata domin bana so na tuna rayuwata ta baya, sai dai a yau zan sanar da ku komai "
Wasu hawaye ne masu zafi sukaci gaba da sakkowa kan kuncinta, tissue ta janyo gami da share hawayen bawai don sun daina zubowa ba, gyara zama su duka sukayi sannan ta fara.

-----------Arewasound.Com------------

------------Arewasound.com-------------

Falon ya d'auki shuru badda k'aran AC da fanka da suke aiki bakajin komi, Farida ce ta katse shurun da cewa.
"please karkusa na k'ware mana duk kunsa min ido" Jidda ce ta ce.
"toh gani mukayi kintsaya cin yanga bayan kinsan ke muke jira" Ita kuwa Maryam murmushi ta yi.

Alokaci guda fara'an kan fuskarta ya juye zuwa damuwa, dubansu ta yi, sannan tace
"Yau zan baku tarihin rayuwata wanda na ke so yazama izna ga y'an baya"
Hawaye ne ya zubo kan kuncinta sannan ta cigaba da cewa "a zahirin gaskiya kune mutane na biyu da ni da kaina na ta6a basu tarihin rayuwata domin bana so na tuna rayuwata ta baya, sai dai a yau zan sanar da ku komai "
Wasu hawaye ne masu zafi sukaci gaba da sakkowa kan kuncinta, tissue ta janyo gami da share hawayen bawai don sun daina zubowa ba, gyara zama su duka sukayi sannan ta fara da: