-Advertisement-

-Advertisement-
Al'adar sayar da mata tun suna kanana, wata al'adace da ta samo asali a wurin al'ummar Becheve, da ke kauyen Obanliku cikin jihar Cross River. Iyaye suna amfani da yara mata wurin musayar abinci, dabobbi, ko kudi. Irin wadannan matan su suke kira da matan kudi.
siyar da mata a internet

Sai dai yanzu wani cigaba da al'ummar yankin suka samu shine, suna amfani da shafin yanar gizo na facebook, wurin tallata 'ya'yan na su. Lokuta da dama akan sayar da su ga tsofaffin mutane, kuma da an sayar da ke, shikenan kin zama tamkar baiwa ga wannan mutumin har bayan rayuwarki.

Mutanen su suke zabar abinda matan zasu yi musu. Wasu suna amfani da su wurin kwanciya, wasu kuma suna mayar da su 'yan aikin gida da zuwa aikin gona, wasu ko zaben suzasu fada miki wanda zaki zaba.

Duba wannan : Hatsarin Mota: Masu Zuwa Shan Maganin Bindiga Zamfara 19 Sun Mutu A Hanya. 

Wata yarinya mai suna Monica ta bayyanawa 'yan jarida yadda mahaifinsu ya sayar da su ba tare da son ransu ba, domin ya biya wani bashi da ake binshi. Monica ta ce ita da kanwarta anyi musu auren dole da mutanen da ba su san su ba, kuma tsofaffi.

Ta ce: "Mahaifinmu bai san da wani abu Facebook ba har sai lokacin da yayanmu ya siyo mishi wayar salula ta zamani, sannan ya roke shi akan ya fara amfani da Facebook, ya na saka hotunan mu a duk lokacin da ya ke so.
"Ya na siyo mana sabbin kaya ya ba mu saka kafin ya dauke mu hoto ni da kanwata."