-Advertisement-
-Advertisement-

Dandalin Fasaha: Yadda Ake Hada Software ; Gabatarwa


Wai Yaya Ake Hada Software?
Software sun zama abokan aiki ga al'umma a zamanin yau, domin duk wata waya ko computer da zaka samu tana aikine da software ko application. Kuma wadannan softwares muna amfani dasu a fannoni dadama. Misali muna aiki dasu wajen kira, da tura sakonni, wasu kuma wajen shiga internet, ko kuma wajen ciran kudi a banki, da kuma more gyama gyamai acikin wayoyin mu da computer da sauran aiyukansu.

DUBA KUMA : Dandalin kimiyya : Sadarwar Satellite

Da farko, yakamata musani ita computer duk wani sako da bayanin da zai shiga cikinta, tana juya shine zuwa wasu lambobi biyu wato 0 da 1 Digits ko kuma muce binary sannan ta ajiyesa. Misali, idan na rubuta NURA a computer, to zata juyashi zuwa binary ne. Zakaga sunan NURA zai koma kaman haka:
N yana daidai da 010011
U yana daidai da 110100
R yana daidai da 101011
A yana daidai da 110010

Sunan NURA zai zama daidai da wadannan lambobin 010011 110100 101011 110010. Hakama duk wani code da za'a rubuta, computer saita juyashi zuwa binary domin shi take fahinta.

Dandalin Kimiyya : Yadda Ake Hada Software ; Gabatarwa

Software ana hadasu ne ta hanyar yaren da mutum yake iya fahinta (programming language) sannan a zubashi a computer. Nace yaren da mutum yake iya fahinta ne, saboda binary yafi wadancan yaren wahalar fahinta, domin shi binary da lambobi biyu kawai ake aiki. Sukuma wadancan yaren ana amfani da lambobi da harufan da basu da adadi. Wadannan yarukan sune Java, da C, da C#, da C++, da Ruby, da Javascript, da SQL, da Perl, da Objective C, da makamantansu. Wadannan sune yarukan da computer take fahinta duk abun da ka rubuta a wannan yaren zata juyashi zuwa binary, sannan tafutar da sakamakon abun da karubuta a screen.

DUBA KUMA : Dandalin kimiyya : Sadarwar Satellite

Bari muyi misali da code mai sauki na wani yare daga cikin wadanda na lissafo asama
#include
int main()
{
std: :count <<"Barka da karatu"; } Wannan code din da na rubuta duk yawansa idan aka saka a conputer zakaga ta rubuta Barka da karatu. Wannan misalin da nayi, nayi ne da yaren C++ mai saukin fahinta. . Lokacin da computer zata juya wannan code din zuwa binary shi ake kira compiling. Hada software kala biyune na farko ana kiranshi proprietary, na biyun shine open source. . Proprietary shine software da aka hada domin a siyarwa wani ko wani kamfani. Open source shine bayan an hada application yayi yawa ansanshi duniya, sai su wadanda suka hadashi, suciro code din da suka hada software da shi su nunawa duniya code din. . Open source yayi tasiri a software da application da muke dasu a yau. Idan kaduba Chrome da Firefox zakaga browser ne masu aiki iri daya. Sai de chrome ta kamfanin Google ce. Bandasu akwai wasu application da zaka samu kalansu daya kusan komai nasu irin daya. Amma suna da dan wani banbanci. Sunan suma ya banbanta. . Kuna iya sharing wasuma sugani su karanta su amfana. 


Rubutawa 
Nura Mahdi Idris