-Advertisement-
-Advertisement-

A DAREN JIYA MISALIN KARFE 2:36 AM


Katsam sai na farka daga bacci sakamakon kullewar da cikina yayi, cikin gaggawa na bude kofar daki na fito zuwa Toilet dake a tsakar gida, idona a rufe yake sadoba cikin da nake ta dannawa, a haka na karasa Toilet, bayan mintuna da basu wuce goma ba, na fito da niyyar komawa daki, sai naji kamar ana kiran sunana, cak na tsaya tare da waigawa bayana da gefe na amma banga mai kiran ba, sai na sake jin ance Rabiu, gabana ya fadi tare da yinkurin kara sauri da niyyar inkai bakin kofar dakin nawa, sai a lokacin ido na yakai kan wani dan karamun mutum da baifi tsawon Gwangwanin Madara ba, kansa katoto sanye cikin kayan da ba zasu misultu ba.
labarin Aljanu
Rabiu magana nake maka, amma kana kokarin guduwa bayan kuma baka da damar da zaka iya gujemun, domin nine dai na kullemaka ciki a cikin dakin naka, nayi hakan ne domin ka fito mu hadu dakai, turoni akayi in tafi dakai, akwai abun daya taso na gaggawa da ake son ganinka yanzu, sai a sannan jikina ya dena rawar da yake, jin da nayi yace aiko shi akayi, sai na zata ko abokin Aljani UNGURAMI ne, sai na tambayeshi ina UNGURAMI dashi baizo ba sai kai aka turo, sai yace inda ake son ganinka ba yankinsu bane, kuma neman da ake maka yana da alaka da alakarka da aljani UNGURAMI da ZIRZARA'U tare da sarkinsu DUNDUS, wannan karon Aljani TUNKURUS ne ke son ganinka cikin gaggawa.

Na bude baki da niyyar inyi magana sai kawai naga ya fito da wani kyalle a hannunsa ya jefoshi jikina, nan da nan sai kawai naji ina silalewa zuwa kasa har na koma yar karamar halittar dashi dan karamin aljanin ya zama kamar giwa a gabana, ina ji ina gani ya daukeni ya saka a cikin wani kwatashi daya fito dashi daga cikin rigarsa ya mayar ya rufe bayan ya sakani a ciki, daganan ban sake sanin abun dake faruwa ba, sai bayan da akasake bude kwatashin aka fito dani sannan na fahimci cewa tuni har ya karasa dani inda ake ce ya kaini.

Cikin zare idanu da waige waige na fuskanci wajen da nake zagaye nake da wasu halittu da sukafi wanda ya daukoni munin gani, suna da siffa kusan irin ta dan adam, sai dai kafafuwansu shida ne a jikinsu suna da hannaye hudu tare da manya manyan kawuna, hancinsu yana da tsawo kamar biro, bakinsu kuwa ya mamaye kusan dukkan fadin fuskar tasu, hakora zako zako tare da harshe a waje, idanunsu jajaye kamar garwashin wuta, bayan dana kare musu kallo daya bayan daya, sannan na fara samun damar magana a wajen inda na tambayi shi wanda ya kawoni wajen, nace masa ai sai ka gabatar dani tunda dai mun iso, sannan wye daga cikin wadannan yan uwan naka yake son ganina da har ya turaka ka taho dani, kafin yakai ga bani amsa sai naji ance Biyoran Baba Buhari na Nigeria dafatan kazo kalau, sannan ina baka hakuri akan wannan gayyata daka samu ba tare da ka shirya ba, zauna a kawo maka abun lasawa tukunna kafin mukai ga sanar dakai dalilin kawoka nan da akayi.

Cikin rashin tsoro na samu waje daya kan wata katifa mai laushi na zauna, kar kuyi mamakin rashin tsoratar tawa, domin na riga na saba da ziyaryar duniyar aljanu tuntuni hakan yasa su kansu wadannan ban tsorata sosai ba, sai shi wanda nake zaton shine babban nasu ya taso ya matso kusa dani, ya fito da wani kyalle daga jikinsa ya karkada shi a saman kaina, sai kawai naga girman jikina ya dawo kamar yadda nake a duniyar mutane, sannan sai yace na mayar dakai karami ne saboda jikinka bazai iya jure doguwar tafiyar da mukayi dakai zuwa nan ba, mun shafe tafiyar sama da kilometers miliyan uku daga duniyarku zuwa nan wajen da muke, kuma kaga cikin kasa da minti biyar mukayi wannan tafiyar.

KADAN KENAN DAGA LABARIN DAYA FARU DANI A DAREN JIYA, LOKACIN DA ALJANU SUKA DAUKENI ZUWA DUNIYARSU.

Rubutawa
Rabiu Biyora