-Advertisement-
-Advertisement-
Sabon shirin Kwana casain 90

A SHIRIN KWANA CHASA'IN NA WANNAN SATIN

Shirin ya fara bayyana kalolin tarin kalubalen da zaa fuskanta a cikin sabon season 2 da aka fara a yau.
Sabon shirin kwana casa in 90
An tabo matsalar jarrabawar Qualifying da dalibai keyi a makarantun Gwamnati don tantance daliban da ita Gwamnati zata biyawa kudin jarrabawa, an nuno dalibai suna duba sunayensu, inda wata hazikar daliba ta kasa cin jarrabawar duk da shaidar da akayi mata na cewa tana daga cikin daliban da sukafi ilmi a makarantar, sai kuma aka nuna gidansu na matsakaitan masu karfi, amma rashin aikinyi na damun mahaifinta, ita kuma mahaifiyarta bata da lafiya, akwai dai tarin kalubale a gidan, na tabbata nan gaba masu shirin zasu fito da cikekken bayani akan wannan gida.

Sai aka nuno sabuwar rayuwar da tsohon Gwamna Bawa maikada yakeyi shida iyalansa a sabon gidan da suke zaune bayan faduwa zabe, Bawa Maikada yana cike da mamakin halayyar daya ke fuskanta ta gujemasa da mutane sukayi tun baa shige kwana Chasa'in da rasa mulki ba, sannan Tsohon Gwamna ya hadu da tashin hankali lokacin da yaje Taaziya inda aka nuno wani talaka yaci kwalarsa tare da tuhumarsa da laifin kashe masa mata zamanin yana mulki, bayan nan dai ya sake haduwa da ihun bamayi akan hanyarsa ta komawa gida, wanda hakan ya sanyashi tunanin kashe kansa, matarsa ta samu nasarar dakatar dashi daga aikata wannan babban kuskuren.

An nuno wani matashi cikin mota yana ganganci tare da yan mata cike da motar tasa, wasu matasa sukayi kokarin ja masa kunne sai aka ga ya gayyato Police sun kame matasan, daga baya kuma aka sake nuno matashin suna shaye shaye tare da yan matan a cikin dakinsa, ashe matashin Dan Gidan Sabon Gwamna Malam Adamu ne, an nuno cewa tsohuwar matar Malam Adamu ta dawo da matashin gidan mahaifinsa wato gidan Gwamnati.

Sabon Gwamnan Alfawa Malam Adamu, an nuna shi a ofis dinsa inda wani Attajirin da yake cika bakin yanzu Gwamnatin tasu ce, yake son gwamna ya saka baki a sakar masa da kayayyakinsa daya shigo dasu Kwastam suka kame, Gwamna Malam Adamu yace bazai saka baki ba, har ma Gwamnan yake bayyana cewa tabbas zai hadu da matsala da mutane a mulkin nasa, domin acewarsa mulkin talakawa ne kuma saboda talakawa zaiyi mulkin.

An nuno Rayya a kauye ana shirin bukinta, amma alamu na muna bata hakura da rayuwar Birni ba, don haka sai gata a cikin mota ta gudo daga kauyen nasu inda ta nufo birni.

A wannan satin a cikin shirin Kwana Chasa'in sharar fage aka fara tare da nunawa masu kallo irin tarin kalubalen dake nauke a cikin wannan shirin da zaa cigaba da haskawa a kowacce ranar Lahadi.

Ni dai shirin ya birgeni, kuma ina kyautata zaton Season 2 zaifi season 1 kayatarwa.....

Kaifa/kefa ya kuka ga shirin na wannan rana