-Advertisement-
-Advertisement-

 Dandalin kimiyya : Menene Optical Fibre Cable ?

Dandalin kimiyya : Menene Optical Fibre Cable ?

- Menene optical fibre cable?
- Bayani Akan Optical Fibre.
- Hotunan Yadda Optical Fibre Cable Yake.


Ka Taki sa'a, Barka Da Kasancewa Da shafin Arewasound.

Kafin mu fara bayanin optical fibre, za mu fara da bayanin menene photon. Photon shine kwayar haske guda daya wanda ba shi da nauyi, sannan kuma ya na gudun kilomita dubu dari uku a duk second daya (300, 000km/s). Wato a cikin second daya photon zai iya zagaye duniya samada sau biyar. Miliyoyin photon ne suke wucewa ta cikin ramin allura wajen da ake saka zare duk a tare kuma a lokaci daya, saboda kankantarsa.

Duba kuma : Dandalin kimiyya : Menene 5G? (Gabatarwa)

Akwai hanyoyi masu yawa da ake amfani da su wajen tafiyar da sakonnin kiraye kirayen wayar salula da sadarwar internet. Wasu hanyoyin ana amfani da tauraron dan Adam (satellite), wasu da turken sadarwa (cell tower) ake aiki, wasu kuma da optical fibre ake aiki, da sauransu. To da yaddar Allah za mu yi bayani game da optical fibre.
Dandalin kimiyya : Menene Optical Fiber Cable ?
Wannan shine misalin optical fibre cable

Optical fibre su ne suke daukan sakonnin kiraye kirayen waya, da sakonnin internet daga wani bangare na duniya zuwa wani bangaren. Optical fibre wani siririn cable ne wanda bai kai kaurin gashin mutum ba. Kuma suna nan an shimfadasu a karkashin kasa, da karkashin teku. Sannan kamfanoni kamansu Google, da AT&T, da Verizon, da Orange ne su ke samar da su.

Wadannan cable din su na daukan sakonin sadarwa ta hanyar hasken da ido ya ke iya gani (visible light), wato su ba kaman satellite su ke ba, domin satellite ya na tafiyar da sadarwa ta hanyar radiowaves (radio frequency) wanda ido ba ya iya gani. Optical fibre sunada tsayin kilomita dari (100km) ko sama da haka. Kuma su suke daukan sakonnin sadarwa masu dumbin yawa daga turai (Europe), zuwa afurka (Africa), ko daga Africa zuwa turai, ko daga Asia zuwa turai, ko daga Africa zuwa Asia, ko Latin America.
 

Yanda abun ya ke, idan ka dauki wayarka, misali, ka shiga WhatsApp sai ka rubutawa abokinka sakon 'slm' ka aika masa. Wayarka za ta juya sakon 'slm' zuwa binary kaman haka 01000 10010 000110 sannan sai ta tura shi cikin iska a matsayin waves. Daga nan sai kwayoyin haske wato photons (amma na radiowaves) su dauki sakon cikin gaggawa su kai shi turken sadarwa mafi kusa da kai.

Shi kuma turken sadarwar ya na karban sakonnin a nan take zai fara kawo wata jar wuta ya na daukewa (light pulses). To a lokacin da ba a amfani da optical fibre a bangaren sadarwa ta wannan jar wutar da idon mu ya ke gani wasu sakonnin su ke tafiya. Shiyasa idan jirgi ya na tafiya za ka ga wata jar wuta a jikinsa ta na kawowa ta na daukewa domin sadarwa tsakaninsa da abokan aikinsa da suke a tashar jirgi (airport). To kuma da aka samu optical fibre wadannan sakonnin su na isowa turken sadarwan a take zai juyasu zuwa haske.

Bayan ya juyasu zuwa haske, sai su shiga ta cikin optical fibre cable su wuce zuwa cibiyar sadarwa. Daman tsakanin turken sadarwa da cibiyar sadarwa akwai optic cable a binne a cikin kasa. Daga nan sai sakonin su tafi wajen wanda aka aikawa sakon a matsayin binary kaman haka 01000 10010 000110 sai wayarsa ta juya masa sakon zuwa harufa kaman haka 'slm' ko da kiran waya ma ta haka ya ke tafiya amma shi wayar sai ta juyashi zuwa sound wave. Sannan miliyoyin sakonni su ke tafiya, haka kuma wannan aikin ya na faruwane kafin kiftawar ido.

Duba kuma : Dandalin kimiyya : Menene 5G? (Gabatarwa)

Optical fibre a da can ana amfani da ita wajen daukan hotunan can cikin cikin mutum (inside human body). Optical cable an yi su ta yanda ba sa tsinkewa, kuma wani abu ba zai iya shiga cikinsu ba. Sannan an rufesu da karafuna masu karfi da kwari kuma an rufe wadannan karafunan da robobi ta yanda ruwa ba zai tabasuba balle suyi tsatsa.


Amma fa a sani kamfanonin sadarwa kaman MTN, ko GLO, ko Airtel duk wanda ya ke so sakonninsa su tafi ta cikin optical fibre cable sai ya biya Google, ko Orange ko AT&T sannan sakonninsa su tafi a cikin optical cable. Optics bangaren physics ne wanda ya ke bayani game da haske a matsayin waves.

Duba kuma : Dandalin kimiyya : Menene 5G? (Gabatarwa)

RUBUWATA
Nura Mahdi IDris