Katsina An kama maza 10 da sukawa 'yar shekaru 14...

An kama maza 10 da sukawa ‘yar shekaru 14 fyade da sakamata Kanjamau a Katsina

-

Jami’an ‘yansanda a jihar Katsina sun kama mutane 10 da ake zargi da yiwa wata yarinya me shekaru 14 fyade da kuma saka mata cutar kanjamau.

 

An yi holin wanda ake zargi, Yau Miko, 40; Taade Nati, 35; Saminu Hashimu, 25; Mannir Yunusa, 35; Danladi Idi, 30, Rabiu Abdu, 40, Burhani Sanda, 30; Isiya Yunusa, 30; Musa Haru, 60; da Shafiu Mamman, a hedikwatar ‘yansandan jihar, rabar Laraba, 18 ga watan Nuwamba 2020.

Yansanda sun bayyana cewa wanda ake zargin sun yiwa yarinyar fyadene a lokuta daban-daban a kauyen Kwadage dake karamar hukumar Mai’adua ta jihar Katsina.

 

Mahaifin yarinyar, Mu’azu Yakubu ne ya kai kara wajan ‘yansanda inda hakan ya kai ga kama wanda ake zargi.

 

An kai yarinyar Asibiti dan bata kulawa.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay you

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

You might also likeRELATED
Recommended to you