Smart News EverydayAREWASOUND
سُبحَانَ اللّهِ وَ بِحَمْدِهِ ، سُبحَانَ اللّهِ الْعَظِيمِ

Breaking News An Kashe Mutane 349 A Cikin Wata Guda A...

An Kashe Mutane 349 A Cikin Wata Guda A Nijeriya

-

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Akalla mutane 349 aka kashe a sanadiyar munanen hare-haren da aka kaddamar a cikin watan Nuwamban da ya gabata a sassan Najeriya kamar yadda wani rahoto da kungiyar ‘Nigeria Mourns’ ta fitar ke cewa.

Gidan rediyon Faransa ya labarto cewa; rahotan mai taken “ Munanan aukuwa” ya yi nazari kan kashe-kashen da aka samu a sassan Najeriya a cikin watan Nuwamba kadai, kuma kingiyar ta Nigeria Mourns ta tattara alkalumanta ne daga jaridu da kuma majiyoyin iyalan mamatan.

Kungiyar ta kewaya jihohin Najeriya 23 domin tattara alkaluman.

Rahotan ya nuna cewa, fararen hula 309 aka kashe daga cikin adadin, yayin da aka hallaka jami’an tsaro 40.
Kazalika rahoton ya nuna cewa, an yi garkuwa da mutane 290 a cikin watan na Nuwamba kadai.
Jihar Borno ke kan gaba wajen yawan asarar rayukan al’umma a cikin watan kamar yadda alkaluman mamatan suka nuna.

Ga cikakkun alkaluman da kungiyar ta fitar:

Borno – 162, Edo – 57, Kaduna – 55, Katsina -12, Delta – 11, Zamfara – 10, Oyo – 5, Ondo – 5, Enugu – 4, Kogi -3, Kano – 3, Ekiti – 3, Adamawa – 3, Bayelsa – 3, Cross River – 2, Nasarawa – 2, Niger – 2, Rivers – 2, FCT – 1, Akwa Ibom – 1, Ebonyi – 1, Ogun – 1 and Sokoto – 1.

Read more at SOURCE: This post (An Kashe Mutane 349 A Cikin Wata Guda A Nijeriya) firstly published at dimokuradiyya.com.ng on 2020-12-22 15:38:58

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

Karanta Wannan:-  Financial details of Odegaard's transfer to Arsenal from Real Madrid

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you

Karanta Wannan:-  Duk da Umarnin kama wanda yace a kori Fulani daga jihar Oyo da IGP Adamu da Gwamna Makinde suka bayar, Kalli Bidiyonsa a gaban 'yansanda da Sojoji yana fadar cewa sai Fulani sun bar garinsu amma ba'a kamashi ba