Smart News EverydayAREWASOUND
سُبحَانَ اللّهِ وَ بِحَمْدِهِ ، سُبحَانَ اللّهِ الْعَظِيمِ

Cristiano Ronaldo Andrea Pirlo ya bayyana cewa zai hutar da Cristiano...

Andrea Pirlo ya bayyana cewa zai hutar da Cristiano Ronaldo a wasan su da Benevento na gasar Serie A

-

Cristiano Ronaldo ba zai buga wasan da Juventus zata kara da Benevento ba ranar sati a gasar Serie A, bayan kocin kungiyar Pirlo ya zabi ya hutar da shi saboda ya bugawa Portugal dama kungiyar baki daya wasannin masu yawa.

Dan wasan mai shekaru 35 ya buga gabadaya wasannin kasar shi guda uku a cikin hutun kwanaki bakwai, yayin da Portugal ta rasa damar kai wasanin karshe na gasar kofin kasashen nahiyar turai bayan da tasha kashi a hannun Faransa.

Andrea Pirlo ya bayyana cewa zai hutar da Cristiano Ronaldo a wasan su da Benevento na gasar Serie A

Ronaldo ya buga gabadaya wasannin Juventus tunda aka dawo hutun yayin daya taimakawa kungiyar da kwallaye biyu a wasan su da Cagliari, sai kuma yaci kwallo guda a wasan da suka lallasa Ferencvaros 2-1 wanda hakan yasa suka cancanci buga wasannin karshe na gasar zakarun nahiyar turai.

Kocin Juventus Andrea Pirlo ne ya bayyana cewa tauraron dan wasan ba zai buga wasan su da Benevento saboda ya kamata ya huta, yayin da Paulo Dybala da Alvaro Morata zasu jagoranci kai hare hare a wasan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay you

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you