Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot
Kungiyar Manchester City tayi nasarar lallasa Arsenal daci 4-1 a gasar kofin Carabao ta hannun Gabriel Jesus wanda yaci kwallon shi ta farko a kungiyar tun a watan nuwamba na shekarar data gabata, sai kuma Phil Foden da Mahrez da Laporte suka zira sauran kwallayen, yayin da shima Lacazette ya ciwa Arsenal kwallon guda.
Sakamakon wasan yasa yasa yanzu Manchester City ta cancanci buga wasannin kusa da karshe na gasar yayin da take shirin lashe kofin gasar karo na hudu a jere. Itama kungiyar Brentford tayi nasarar kai wasannin kusa da karshe na gasar karo na farko a tarihi bayan ta lallsa Newcastle daci 1-0.
Manchester City ta zamo kungiya ta farko data yi nasarar cin wasannin daba na gida ba guda hudu tsakanin ta da Arsenal tun bayan Chelsea tsakanin shekara ta 1960 zuwa shekara ta 1965, wadda ita tayi nasarar cin wadanni shida a jere tsakanin ta da Arsenal din.
Kungiyar Arsenal tasha kashi daci biyar a wasan gida na gasar kofin Carabao karo na farko tun shekara ta 1998 a lokacin da Arsene Wegner yake jagorancin kungiyar, yayin da Chelsea ta lallasa su daci 5-0.
Labarai masu alaka
Read more at SOURCE: This post (Arsenal 1-4 Manchester City,Brentford 1-0 Newcastle: yayin da Manchester da Brentford suka cancanci buga wasannin kusa da karshe na gasar kofin Carabao) firstly published at hutudole.com on 2020-12-22 22:42:12
Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot
Thanks for visiting Arewasound.com