Connect with us
Ramadan KAREEM

Labarai

Babbar Alkalin Nasarawa ta yi wa fursunoni 47 afuwa

Published

on

Babbar alkalin jihar Nasarawa, Mai shari’a Aisha Bashir, ta yi afuwa ga fursunoni 47 na gidajen yarin gwamnatin tarayya da ke Lafia, Keffi, da Nasarawa, wadanda ke jiran shari’a.

Aisha ta bayyana haka ne a ranar Alhamis a karamar hukumar Wamba bayan rangadin cibiyoyin kula da su a ranar Alhamis, NAN ta ruwaito.

”Ziyarar ta yi daidai da umarnin da fadar shugaban kasa ta bayar ga masu karamin karfi a wani bangare na matakan dakile yaduwar COVID-19.

”A karkashin duba na, bangaren shari’a a jihar zai yi aiki don tabbatar da hanzarta gudanar da shari’a tare da magance matsalar rashin adalci.

”Kwamitin shari’ar masu aikata manyan laifuka a jihar nan ba da jimawa ba zai fito da hanyoyin da za su tabbatar da cewa wadanda shari’ar tasu ta kasance tsawan shekaru ba tare da ci gaba ba za a kammala shari’unsu kuma a gabatar da adalci.

“Na kuma nemi da a tattara sunayen fursunonin da suka kwashe shekaru biyar zuwa sama don gabatar da su ga Gwamnan Jihar na gaba don yafiya.

Ta kara da cewa “Muna ba da shawarar ga gwamnan da ya yi musu afuwa a matsayin wani bangare na kokarin tabbatar da yin adalci kamar yadda ya dace.”

Ta kuma taba wa hukumomin Cibiyoyin hukumar saboda koyar da fursunonin sana’o’i daban-daban da shigar da masu sha’awar neman ilimi a Jami’ar Open.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


CHECK OUT
[related_posts_by_tax]
How to Setup Glo Unlimited Browsing 2021

Airtel Bonus Code You Can’t Miss 2021

SOURCE: This post (Babbar Alkalin Nasarawa ta yi wa fursunoni 47 afuwa) firstly published at www.hutudole.com on 2021-04-08 13:03:51

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Copyright © 2012 Present | Powered by AREWASOUND LTD.