LabaraiBarcelona zata kara tsawaita kwantaragin Pedri Gonzalez

Barcelona zata kara tsawaita kwantaragin Pedri Gonzalez

-

A cewar wani rahoto daga dan jaridar nan na Italiya Fabrizio Romano, Barcelona na son tsawaita kwantiragin matashin dan wasan ta mai shekaru 18 Pedri Gonzales. Kungiyar ta dauke shi dan wasa na musamman kuma suna son fitaccen dan wasan ya zauna a kungiyar na dogon lokaci.

Kwantiragin sa na yanzu zai kare a karshen kakar wasa me zuwa ta 2022. Duk da cewa ya tabbata zai ci gaba da zama, Barcelona na shirin ba shi sabon kwantiragi.

Barcelona tana da zaɓi na tsawaita yarjejeniyarsa da ƙarin shekaru biyu, kuma ta nemi ta ba shi ƙarin albashi, amma da zarar an daidaita daga halin matsin rashin kuɗi da kungiyar take fuskanta. #Continue Reading>>

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you