Ayo Salami Be kamata sabon Shugaban EFCC na Gaba ya fito...

Be kamata sabon Shugaban EFCC na Gaba ya fito daga bangaren yan sanda ba>>Mai Shari’a Salami

-

Advertisements
Advertisements

Justice Ayo Salami, shugaban kwamitin da aka kafa domin binciken zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yiwa Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Ibrahim Magu, ya ba da shawarar cewa be kamata sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ya fito daga rundunar ‘yan sanda.

Ya bayar da wannan shawarar ne a ranar Juma’a, bayan ya gabatar wa da Shugaba Muhammadu Buhari rahoton kwamitin da aka kafa don binciken zargin cin hanci da rashawa da Babban Lauyan nan kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, keyi akan shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu.

 

A cewarsa, shugabannin hukumar EFCC hudu da suka gabata sun fito ne daga rundunar ‘yan sanda ne, don haka ya kamata a ba da dama ga mutane daga wasu jami’an tsaro ko jami’an tsaro kamar yadda dokar EFCC ta kafa a 2014.

Advert

 

Mai Shari’a Salami ya yi imanin da cewa wannan zai taimaka wa hukumar wajen kawo sauyi da ingantaccen aiki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay you

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

You might also likeRELATED
Recommended to you