Connect with us
Ramadan KAREEM

Breaking News

Bodo Illgner: Toni Kroos na da ban mamaki

Published

on

Tsohon mai tsaron ragar Real Madrid Bodo Illgner ya jinjina wa Toni Kroos saboda kwazon da ya nuna a wasan da Los Blancos ta doke Liverpool wasan dab da kusa dana karshe a daren Talata. Fagenwasanni.com ta rahoto.

Bodo Illgner: Toni Kroos na da ban mamaki

Kroos shi ne ya taimaka wa Real Madrid a wasan farko da kwallo daya ban haushi bayan bugun kwallo daga tsakiyar fili, kuma tsohon mai tsaron ragar ya ajiye yabo na musamman ga dan kasarsa.

Illgner ya fadawa Rediyo MARCA cewa “Kroos yana yin komai cikin sauki kuma da alama yana yin hakan ba tare da nuna shi yai kokari kokari ba.”

“Sau da yawa yakan zama kamar bai yi gumi ba.

“Yana da kwarewa sosai kuma yana jin dadi sosai da kwallon.

“Yana da ban mamaki da dogayen saitin bugun kwallaye, a kan kusurwa.”

Illgner ya kuma yaba da aikin Vinicius Junior, wanda yayi imanin yana da karfin gaske.

“Vinicius yaro ne mai tarin baiwa,” in ji shi.

“Gaskiya ne cewa a Real Madrid abin kawai da ake lasaftawa shi ne idan kana da kokari ko a’a, shekaru ba shi da wani muhimmanci, amma wani lokacin sai ka yi haƙuri da matasa ‘yan wasa.”


CHECK OUT
[related_posts_by_tax]
How to Setup Glo Unlimited Browsing 2021

Airtel Bonus Code You Can’t Miss 2021

SOURCE: This post (Bodo Illgner: Toni Kroos na da ban mamaki) firstly published at fagenwasanni.com on 2021-04-08 00:49:18

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Copyright © 2012 Present | Powered by AREWASOUND LTD.