Labarai Buhari Ya Yi Kira Ga Hadin Kan Kasashen Duniya...

Buhari Ya Yi Kira Ga Hadin Kan Kasashen Duniya Don Kawo Karshen Cutar Tarin Fuka

-

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga kasashen duniya da su yi aiki tare da kokarin sake sadaukarwa, ta hanyar amfani da sabuwar fasahar zamani da kayan aiki, don magance annobar tarin fuka (TB), daya daga cikin abubuwan da ke haifar da mace-mace a duniya shine Tarin Fuka, a cewar wata sanarwa daga Fadar Shugaban Kasa ta fitar ranar Alhamis.

Buhari ya yi wannan kiran ne a cikin sakon fatan alheri zuwa ga taron karawa juna sani na Kwamitin “Global Stop TB Partnership”, inda ya nuna damuwarsa cewa kokarin da ake yi na kawo karshen wata cuta da za a iya kawar da ita kamar ta tarin fuka a yanzu tana da rikitarwa saboda COVID-19.

Advertisements

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay you

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

You might also likeRELATED
Recommended to you