Labarai Buri na shine Messi yayi ritaya a kungiyar Barcelona>>Pep...

Buri na shine Messi yayi ritaya a kungiyar Barcelona>>Pep Guardiola

-

A karshen makon daya gabata manajan Manchester City Pep Guadiola ya rattaba hannu a karin kwantirakin shekaru biyu da kungiyar tayi mai, wanda hakan yasa ake rade reden cewa yaznu zai mayar da hankulan shi wurin siyan Messi daga kungiyar Barcelona.

Amma a bayanin da manajan yayi ya bayyana cewa burin shi bai wuce ace Messi yayi ritaya a kungiyar Barcelona ba, inda yake cewa “Messi dan wasan Barcelona ne, kuma ni mutun ne wanda yake girmama kungiyar sosai saboda irin kyautatawar da suka yi min a matsayin da wasa”.

“Saboda haka a matsayina na masoyin Barcelona zan so ace Messi ya cigaba da wasa kuma yayi ritaya a kungiyar, amma sai dai bamu san abinda yake cikin ran shi ba saboda kwantirakin shi zai kare a wannan shekarar”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay you

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

You might also likeRELATED
Recommended to you