Cristiano Ronaldo Cristiano Ronaldo yana daf da zama dan wasan daya...

Cristiano Ronaldo yana daf da zama dan wasan daya fi zirawa kasar sa kwallaye masu yawa a tarihi

-

Tauraron dan wasan Juventus,Cristiano Ronaldo yana daf da zama dan wasan daya fi zirawa kasar sa kwallaye masu yawa a tarihin wasan kwallon kafa kuma yanzu kwallaye bakwai ne suka rage mai ya kafa wannan tarihin.

Ali Deai shine ya kasance dan wasan daya fi zirawa kasar sa kwallaye masu yawa a tarihi bayan da yayi nasarar cin kwallaye har guda 109 da kasar sa ta Iran, yayin da shi kuma kaftin din Portugal, Ronaldo ya biyo bayan shi da kwallaye 102.

Cristiano Ronaldo ya taba cin alwashi karya wannan tarihi na Ali Daei wanda ya dauki tsawon shekaru 14 ba tare da wani dan wasa ya kusanci karya shi ba har sai wannan karin, inda yake cewa “Babu tarihin da ba’a karyawa kuma nima inda daf da karya wannan tarihin”.

Advert

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay you

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

You might also likeRELATED
Recommended to you