ASUU Da wuya mu janye yajin aiki a wannan shekarar>>ASUU

Da wuya mu janye yajin aiki a wannan shekarar>>ASUU

-

Kungiyar Malaman Jami’a ta ASUU ta bayyana cewa irin yanda gwamnatin tarayya ke wa maganar bukatunsu rikon sakainar kashi da wuya a janye yajin aikin da suke a wannan shekarar.

 

ASUU ta kuma bayyana cewa Gwamnatin na wasa da Ci gaban rayuwar matasa inda tace Ikirarin gwamnati cewa IPPIS zai magance matsalar rashawa da cin hanci a jami’o’in Najeriya ba gaskiya bane.

 

Advertisements

Hakan na kunshene a cikin sanarwar da Uzo Onyebinama, ko’odinata na yankin Fatakwal ya fitar. Ya kuma bayyana cewa suna takaicin yanda dalibai suka yi Asarar zangon karatu har 2.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay you

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

You might also likeRELATED
Recommended to you