Dandalin KimiyyaDandalin kimiyya : Menene 5G? (Gabatarwa)

Dandalin kimiyya : Menene 5G? (Gabatarwa)

-

  Menene 5G? (Gabatarwa)

  Barka, Kuna a shafin Arewasound ne. 

  Na lura tun bayan kaddamar da network ɗin 5G, wasu mutane su na ta korafin cewa 5G ya na da illa ko cutarwa ga lafiyar dan Adam ko sauran halittu masu rayuwa a doron kasa (earth) kaman dabbobi. Ba wai a Nigeria ko Africa ne kadai ake wannan korafin ba hatta turai (Europe) da yankin gabashin duniya (Asia) ana wannan korafin. To da ikon Allah za mu yi bayanin menene network din 5G, da amfanoninsa, da kuma dalilan kirkirosa, sannan a bayani na gaba za mu duba shin da gaskene ya na da cutarwa ga lafiya, ko kuma a’a?

  Wannan bayanin ya na matsayin gabatawar ne akan 5G, saboda sauran bayanan su na tafe, idan Allah ya so su din ma za mu yi bayaninsu daki-daki.

  Menene 5G Network?

  5G a takaice ya na nufin Fifth Generation, ko kuma Fifth Generation Of Network. Wato ya na nufin generation na biyar a daga cikin hanyoyin samar da sadarwar zamani. 5G shi ne network mafi karfi da sauri a yanzu haka, sannan kuma ana tsammani ma fi yawa daga cikin sabbin wayoyin da za su zo da shi a cikinsu sai a shekara mai kamawa ta 2021 za su futo, ko kuma karshen shekaran nan.

  Duba Kuma : Dandalin Fasaha : Yadda Ake Hada Software ; Gabatarwa

  Ko-da-ya-ke a yanzu hakama akwai wayoyin Android masu version din Android Pie (Android Q) da Android 10 ma su aiki da 5G. Wadannan wayoyin su ne Google Pixels, da Nexus, da Samsung wadanda ake ganinsu a matsayin kishiyoyin wayoyin iPhone da iPad ne.

  Dalilan kirkiro 5G Network

  Bayan gama bayanin menene 5G a takaice, za mu ci gaba da bayani akan dalilan kirkirosa. Sanin kowa ne cewa a shekarun baya da tarho (telephone) ake amfani wajen kiraye kiraye. Kuma shi tarho sadarwarsa ta na samuwane ta hanyar wata igiyar wayar lantarki (wire) wanda ake jonawa ajikinsa, sannan zuwa wani ko wasu tarho din.

  Kenan a shekarun baya ba a cika amfani da electromagnetic radiation a fagen sadarwa ba, sai dai igiyar wayar lantarki, wanda ba ta iya tafiyar da sakonni ma su dimbin yawa, kaman electromagnetic radiation. Saboda haka sadarwar tarho ana iya kiranta generation na farko wajen sadarwa wato 1G, amma fa kafin kirkiro wayoyin salula.

  Bayan kirkiro wayoyin salula sai aka fara amfani da electromagnetic radiation wajen tafiyar da sakonnin sadarwa musamman Radio frequency (RF). Wadancan wayoyin wasu su na la’akari da su cewa su ne generation na farko (1G) a fagen sadarwa maimakon tarho. Wayoyin da aka kirkiro a wancan lokacin aikin sadarwa guda biyu kawai su ke yi. Wato daga kira sai aika gajeren sakon kar-ta-kwana ko kuma SMS a turance. Ana cikin amfani da su a haka sai mutane su ka ga cewa ya kamata wayoyin hannu su kasance ban da kira da sakon SMS, su na iya yin wasu aiyukan.

  Wannan ya sa aka kara kirkiro wasu bangarori a waya da za su taimakawa mutum wajen rage ma sa wasu aiyuka musamman aikin ofishi (office), ko shago. Daga nan sai aka kirkiro bangarori kaman agogo domin ganin lokaci, kalanda domin sanin kwanan wata, Calculator domin yin lissafi, Alarm da Reminder domin tunatarwa, FM Radio domin sauraren labarai, Notes kuma domin yin rubutu da ajiyesa, tocila domin samun haske da dare ko a waje mai duhu, Voice Recorder domin nadar sautin murya da sauransu.

  To ganin cewa wayar salula ta na da wadannan bangarorin sai aka fadada harkokin sadarwarta ta yanda za a iya aika sakon murya wanda aka nada (recording) a cikin wayar. Wannan ya sa aka fadada wayar salula bayan sakon SMS, sai aka kirkiro sakon MMS, wanda ake tura sakon murya da sakon rubutu mai yawa. To wadannan wayoyin su ake ganin cewa su ne generation na sadarwa na biyu wato 2G.

  Bayan yawaitar wayoyin Sagem da Nokia da Motorola da Samsung da sauransu wadanda ana iya kiransu wayoyin zamani – saboda su bayan nadar sautin murya za su dauki hoto da kuma hoton bidiyo, ga kuma wasanni (games). To bayan wannan sai aka fara tunanin fadada waya ta yanda za ta iya shiga yanar-gizo, su dai wadannan wayoyin wato Nokia, da Samsung, da Motorola, da Sagem da makamantansu sai aka fadada fasaharsu wanda za su shiga internet da ita. To wadannan wayoyin su ne tushen generation na uku wato 3G.

  Daga nan sai wayoyi su ka yawaita a hannun mutane, sannan sadarwa wato network ya zamo ba shi da sauri ko karfi. Daman a wancan lokacin wayoyi su na amfani da satellite ne da kuma turken sadarwa domin samar da sadarwa. Turken sadarwa wani dogon karfene kaman ka’inji da za ka ga jikinshi an yi masa jan fenti (red) da fari (white). To mutane sun yi yawa kuma bukatar shiga internet ma ta karu, dalilin haka sai aka kara adadin yawan satellite din da su ke cikin sarari su na aiki, da kuma rage nisan da ke tsakanin turken sadarwa ta hanyar kara kafa wasu turakun sadarwa. Dalilin kokarin fadada 3G aka samo 4G.

  Shin 5G ya na cutarwa ga lafiya?

  5G ba ya cutarwa ga lafiya, saboda ya na amfani da electromagnetic radiation wadanda ba sa cutarwa wato radiowaves da visible light ne. Su visible light da radiowaves frequency na su ba su da cutarwa ga lafiyar dan Adam. Visible light shi ne hasken da mu ke gani da shi, shi kuma radiowaves daman da shi ake amfani wajen sadarwar rediyo da talabijin, kuma shi ne radiation ma fi rauni a cikin electromagnetic radiation.

  Za mu dakata a nan, idan Allah ya sa mu na raye za mu ci gaba da bayani akan aikin 5G.

  Duba Kuma : Dandalin Fasaha : Yadda Ake Hada Software ; Gabatarwa

  Rubutawa:

  Nura Mahdi Idris.

  Publishing on Arewasound by :
  Abdullahi Hashim Abdullahi.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here

  - Advertisement -

  You might also likeRELATED
  Recommended to you