Connect with us
Ramadan KAREEM

Dandalin Kimiyya

Dandalin kimiyya : Menene Aerodynamics?

Published

on

Menene Aerodynamics ?

Aerodynamics wasu kalmomi biyu ne, aka hada suka bada  wannan kalma. kalma ta farko (Aero) yana nufin abun da yashafi iska(air) ko kuma iskar kan ta, kalma ta biyu (Dynamics) yana nufi motion na abu da kuma forces (karfi) nashi.

Dandalin kimiyya : Menene Aerodynamics?, Menene Aerodynamics

A takaice dai Aerodynamics yana nufin kimiyar tafiyar abu acikin fluid. Idan akace fluid ana nufin abu kaman iska ko ruwa. Fahimtar wannan kimiya tabada gudunmuwa wajen tafiyar da kayan sufuri acikin iska, da cikin teku, da kuma cikin sararin samaniya kaman jirgin sama da jirgin ruwa na yaki.

A duk lokacin da abu yake tafiya acikin fluid dole ne zaka samu yana fuskantar kalubale ko turjiya(resistance) daga wannan fluid din. Kaman yanda nayi bayani asama idan akace fluid ana nufin abu kaman ruwa ko kuma iska. To lokacin da abu yake tafiya acikin fluid zaka samu yana fuskantar kalubalen da zaisa karfin gudunsa ya ragu.

DUBA KUMA : Dandalin Kimiyya : Menene Friction?

Misali idan kana tuka mota daga gabar kayi yamma. Sai a lokacin kuma iskar daga yamma take tanayin gabar. Kaga kenan wannan iskar tana kalubalantar tafiyar motarka. To jirage ma yayin da suke tafiya acikin iska suna fuskantar irin wannan barazana da kalubale, wanda hakan zaisa jirgin yayi descend.

Descend yana nufin gudun jirgi yarage, wanda zaisa yafado kasa. Aerodynamics ilimin kimiyane wanda gaba daya yana bayanin tafiye tafiyen abubuwa acikin fluid. Samun wannan ilimin yakawo cigaban sifirin sararin samaniya da tafiyar da jiragen ruwa kaman nuclear submarine wato jirgin ruwan yaki da mutane masu nutso a teku wadanda ake kira divers.

Idan muna biye da kafafen yada labarai, wasu lokutan zamuji an sanarda cewa tafiye tafiyen jiragen da aka tsara an sokesu saboda matsalar yanayi. Wannan yana faruwa ne saboda ana tunanin karfin iskan yayi yawa wanda zaisa asamu matsala yayin da jirgi yake sama, ko kuma jirgin yabace gaba daya daga taswiran masu kula da shi.

Aerodynamics bawai jirgin ruwa da jirgin samane kadai yake magana akai ba – hatta mota da mashin da keke da suke tafiya akan titi suma haddasu, saboda akan titin ma akwai iska.

DUBA KUMA : Dandalin Kimiyya : Menene Friction?

Abun dayasa nake bada misali da submarine wato jirgin ruwa na yaki, shine shi submarine yana iya kwanaki casa’in(90days) ko sama da haka acikin ruwa idan ya nitse bai leko sama ba. Kuma yana iya yafiya acikin ruwan bayan ya nutse kaman yanda kada(crocodile) take tafiya bayan ta nitse acikin ruwa, yanda ba’a gane cewa akwai wani abu acikin wannan ruwan.

Rubutawa
NURA MAHDI IDRIS

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Copyright © 2012 Present | Powered by AREWASOUND LTD.