Connect with us
سبحان الله وبحمده سبحان الله العظيم

Dandalin Kimiyya

Dandalin kimiyya : Menene Energy?

Published

on

Menene Energy?

Kaman yanda muka sani mu mutane muna bukatar karfi ko kuzari kafin mu gabatar da wani aiki. Hakama kowane abu yana bukatan karfi kafin yayi nashi aikin daya saba. Wannan karfin da abubuwa suke bukata kafin suyi aiki shi ake kira Energy.

Energy yana nufin karfi ko kuzari da ake bukata kafin ayi aiki. Aikin da ake nufi anan shine kaman yin tafiya, ko yin wani aiki da gabobi. Kwan wutar lantarki(light bulb) yana bukatan karfi kafin yayi aiki. Kwan wutan lantarki aiyuka biyu yake yi, aikin farko shine haske(light), na biyu kuma shine yin zafi(heat).

Energy in hausa, Dandalin kimiyya : Menene Energy?
Dandalin kimiyya : Menene Energy?

Hakama mutum kafin yayi kowane aiki yana bukatar karfi. Wannan karfin mutum yana samune daga abinci da ruwa(chemical energy). Radio kafin yayi aikinshi wato labarai yana bukatan battery(electrical energy). Kwan wuta yana bukatan wuta kafin yabada haske ko yayi zafi. Wannan karfin yana samun sa ne ta hanyar battery da generator da wutan NEPA. 

Motoci da mashina da jirage suna bukatar karfi kafin suyi aikinsu wannan karfin suna samunshi ne daga mai(fuel) da ake saka musu(chemical energy). Wuta(fire) tana bukatar ice da katako da sauran makamashi kaman kalanzir da fetur domin tayi aikinta.

DUBA WANNAN : Dandalin Kimiyya : Menene Atom?

Computer da wayar hannu da MP(media player) da agogo da sauran na’urori suna bukatar karfi kafin suma suyi nasu aikin. Suma karfin nan suna samu ne ta hanyar battery da wutan lantarki.

Principle Law Of Conservation Of Energy
Wannan principle din yana cewa energy ba’a kirkiro shi, hakama ba’a asarar shi a banza. Sai de acanja shi daga wannan nau’in zuwa wani nau’in. Misali idan kudi energy ne. Kaje kayi aiki aka biyaka kudin aikin ka. Sai a hanyar ka ta dawowa gida kudin yafadi a kasa. Kai awajen ka kayi asarar kudin, amma wani zai tsinci kudin yayi amfanin shi da kudin. Kaga kenan kai kudin awajen ka halaliyar kane, wanda kuma ya tsinta a wajenshi kudin tsuntuwa ne. Abun danake nufi shine ba’ayi asarar kudin gaba daya ba. Karasa kudin bakayi amfani dashi ba, amma wani yasamu kuma yayi aiki dashi.

Ire iren karfi
1. Heat(thermal) energy
2. Light energy
3. Sound(acoustic) energy
4. Nuclear energy
5. Magnetic energy
6. Electrical energy
7. Chemical energy
8. Mechanical energy
9. Gravitational potential energy
10. Elastic Energy

1. Heat/Thermal Energy
Heat ko ace Thermal yana nufin zafi. Wannan nau’i na karfi yana da amfani sosai ga rayuwar mu ta yau da kullum. Kuma mafi yawa muna samun wannan karfin ne ta hanyar Rana(Sun) da wuta(fire).

Kadan daga cikin amfanin zafi da kowa yasani shine ana amfani dashi wajen girke girke(cooking) da soye soye(frying) da guga(ironed). Bayan haka ana amfani da zafi wajen hada chemical reaction.

Banan kadai ba wajen narkar(melting) da karafa(metals) a kamfanoni da masana’antu ana amfani ne da zafi. Masu gyare gyare kaman gyaran Radio, da waya, da computer suna amfani da zafi domin narkar da dalma. Makera suna amfani da zafi wajen narkar da dalma da azurfa domin hada tukwane(pots), cokula da ludayi(ladle and spoons) da zobina(rings).

DUBA WANNAN : Dandalin Kimiyya : Menene Atom?

Zafi yana da matukar mahimmanci ga rayuwar dan Adam. Hatta jikin dan Adam kanshi yana bukatar zafi ko da ba mai yawa ba. Wajen sadarwa ta infrared ana amfani da zafi. Sadarwar infrared wata sadarwace da akeyi tsakanin wata na’ura zuwa wata. Kaman tsakanin remote da talabijin, ko tsakanin receiver ta satellite da remote, ko tsakanin remote da video ko mp(media player). A shekarun baya kafin Bluetooth yayi yawa wayoyi ta infrared suke ture ture kaman tura waka da video da hotuna da applications.

2. Light Energy
Light energy nau’ine na karfi da muke bukata domin mu kalli ababen da suke kusa da na nesa damu. Wannan nau’in karfi gaba dayansa shima ana samun sane ta hanyar Rana(Sun) da sauran abubuwan dake ba da haske.

Ana amfani da haske wajen hada chemical reactions. Hakama na’urorin daukan hoto(camera) suna amfani da haske domin dukan hoto mai kaloli(colours). Haske da zafi ababene masu matukar amfani sosai. Ana amfani da haske wajen sadarwa da dai sauran amfanoni wadanda bamu lissafo ba.

Alhamdulillah, mun faro bayani amma zamu tsaya anan mu cigaba akan na uku idan Allah yasa muna raye. Kuna iya turawa wasu suma su karanta su amfana.

RUBUTAWA
Dalibin Physics
Nura Mahdi Idris

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Copyright © 2012 Present | Powered by AREWASOUND LTD.