Dandalin KimiyyaDandalin Kimiyya : Menene Friction?

Dandalin Kimiyya : Menene Friction?

-

Menene Friction?

Friction dai yana faruwa ne yayin da wani abun yake tafiya akan wani abu ko kuma wani abu yana tafiya yake shafar wani abun. Kasancewa abu yana juyawa ko tafiya sannan kuma wani abun yana shafarsa, zaisa saurinsa ya ragu saboda friction.

Friction wani karfi ne dayake baiyana atsakanin abubuwa guda biyu ko sama da haka yayin da suke tafiya ko juyawa suke taba junansu. Ababen hawa ko sufuri na zamani da suke tafiya zaka samu cewa suna fama da friction.

Friction yana rage saurin abu, kuma yanasa sassan injin wannan abun suyi zafi – saboda suna taba junasu. Haka kuma zaisa ko da karfe ne idan ba’a saka masa mai(kaman grease da engine oil) ba zakaga wannan karfen yayi saurin gogewa sannan ya karye.

DUBA KUMA : Dandalin kimiyya : Menene Gravity

Mu dauki misali akan injin mota ko mashi, duba dacewa mafi yawa daga cikin wadannan injinan anyisu ne da karfe – zakaga shiyasa ake lubricating nasu(wato saka musu mai ko shafa musu mai). Kuma zakaga wannan man din da ake sawa adadin sa yana raguwa bayan wani lokaci, kuma yanayin duhu. Yana raguwa ne saboda karafunan suna taba junansu, sannan suyi zafi sai man ya kone, sannan aduk lokacin da suka taba junansu sanadiyar friction dake tsakaninsu zasuyi datti.

Idan muka duba piston zamuga cewa yanada siffar cylinder wato siffar kofin shan ruwa. Sannan ramin dayake ciki shima yana da wannan siffa. Piston yanayin gaba sannan yayi baya acikin wannan ramin hakan zaisa jikin piston din yana shafar jikin ramin. Sanadiyar gaba da baya da piston yakeyi acikin wannan ramin zaisa da piston din da raminsa suyi zafi – kuma suyi kara(noise). Amma dayake bakin mai(engine oil) da ake sawa yana shiga wannan wajen zakaga wannan zafin yarage sosai kaman babu shi, kuma piston din zaiyi aikin sa lafiya kalau ba wata hayaniya; ba wata matsala.

Tsakanin kashi da kashi(bones) musamman wajen gaba(joint) ajikin mutum ko dabba nan ma akwai friction. Amma kasancewa akwai wani mai ko ruwa da jikin mutum ko dabba yake samarwa ya kuma aikashi duk wata gaba, shiyasa zakaga kana motsa gabobinka yanda kakeso batare kaji suna kara kaman wheelbarrown da ba’a samata grease ba.

Misali idan kasamu wani karfe kana gogashi akan wani karfen – zakaji sunayin kara(noise) kuma sunayin zafi yayin da kake gogawa. Amma idan kasa mai ko grease sannan ka goga wannan karfen zakaji karfen yana tafiya mai kyau baya wata kara, hakama basa zafi.

DUBA KUMA : Dandalin kimiyya : Menene Gravity

Kasancewa akwai friction atsakanin takalmi da kasa(ground) shiyasa mutum yake tafiya batare da yafadi ba. Hakama friction dake tsakanin taya da kwalta yana taka muhimmiyar rawa wajen tsayar da mota ko mashin yayin da kataka burki(brakes).

Wannan yasa zaka samu jikin tayoyi akwai kaushi ko zane wanda zaisa burki yayi aiki. Idan taya tsufa, wato wadannan kaushi suka fara gogewa zakaga karfin burkin yarage. A takaice dai friction yana kalubalantar motion ne.

Daga karshe muna barar addu’arku ga dan uwa Malan Real Zaharaddeen M Kt akan Allah yabashi lafiya.

RUBUTAWA
Dalibin Physics
Nura Mahdi Idris

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you