bincikeDandalin kimiyya : Menene GPS Satellite ?

Dandalin kimiyya : Menene GPS Satellite ?

-

Dandalin kimiyya : Menene GPS Satellite?

GPS yana nufin Global Positioning System. Wato wani tsari ne, ko fasaha da ake amfani da satellite domin a gano inda wani ko wani abu yake akan doron kasa a cikin duniya nan. GPS ya samo asali ne daga wani shiri da gwamnatin Amurka tayi wanda zai taimakawa sojojin ta suyi aiki a ko ina a doron kasa, da kuma gano wasu abubuwa masu alaka da tsaro da sauran bayanai.

Amma a shekarar 1980, gwamnati ta bawa mutane farar hula dama suyi amfani da GPS inde suka mallaki na’urar – akwai GPS na hannu yana nan kaman wayar salula.

GPS yana lissafa kwanaki (days), sa’o’i (hours), mintuna (munites) dakiku (seconds). GPS yana bada kwanan wata daidai. Sannan yana iya sanar da kai cewa lokaci kaza ka fara tafiya, lokaci kaza ka tsaya, kuma kayi tafiyan nisan kilomita kaza, kayi minti kaza da second kaza kafin kaje inda za kaje inde kana da GPS receiver a wajen ka.

DUBA KUMA : Dandalin kimiyya : Yadda Drone Yake Aiki

Hatta kai da kake karanta wannan rubutun GPS yana iya fada maka cewa kana kasa kaza, jaha kaza a gari kaza, kuma kana cikin layi na kaza, sannan kana zaune a daidai nisan kilomita kaza tsakanin ka da tsakiyar garin ku, ko gidan gwamnatin garin da kake.

Akwai satellite sama da guda talatin wadanda gano inda wani mutum ko wani abu yake a doron kasa shine aikin su. GPS satellite suna sama a nisan kilomita dubu ashirin (20, 000kilometres) tsakanin su da doron kasa. GPS satellite suna amfani da network domin sadarwa tsakanin su da manya da kuma kananun na’urorin GPS da suke hannun mutane, domin nunawa mutum inda yake da kuma sanin nisan tafiyar kilomita nawa yayi.

Akwai kananun na’urorin GPS na hannu, wadanda mutane suke siyowa suna amfani da su, wajen gano hanya. Wadannan kananun GPS din ana kiran su GPS receiver. A cikin wayoyin hannu na zamani kamansu Android, da iPhone akwai irin wannan fasaha wato Maps, ko Google maps. Wanda take nunawa mutum hanya a cikin wayar sa.

An harba GPS satellite na farko a shekarar 1978.

Sannan kowanne daya daga cikin su ana tsammanin zaiyi aiki na tsawon shekaru goma. GPS satellite yana da nauyin pound dubu biyu (2,000lbs) a takaice, daidai da nauyin kilogram dari tara da bakwai (907kg). GPS satellite yana da solar panel masu tsayin kafa sha bakwai (17 feet) daidai da tsayin mita biyar da wani abu (5metres) wadanda suke samun wuta daga hasken rana – kuma su suke samarwa GPS satellite wutar lantarki.

Bayanan GPS satellite suna tafiya ta cikin hadiri ko giza gizai, da ruwa ko iska, da kuma ta cikin glashi ko roba – sannan GPS satellite yana da karfin aiki (power) na watt hamsin (50 Watts) ko kuma abun da baikai haka ba.

GPS satellite suna zagaye duniya sau biyu a kullum. Sannan kuma a takaice suna gudun mile dubu bakwai duk sa’a daya (7000mph), daidai da gudun kilomita dubu sha daya da dari biyu da sittin da biyar (11265kmph).

DUBA KUMA : Dandalin kimiyya : Yadda Drone Yake Aiki

GPS satellite guda uku ne suke iya gano inda wani abu ko wani mutum yake a doron kasa. Sannan kuma sai sun zama su hudu ne suke iya samar da cikakkun bayanai akan duk abun da suka hango a doron kasa – daga nan sai su samar da sauran bayanai kaman gano nisan da abun yayi, da kuma saurin abun a lokacin da yake tafiya da kuma daidai inda yake, tare da kwanan wata.

GPS satellite kaman kowane satellite suma suna aika bayanai ta hasken da idon mutum baya iya gani, wato Radiowaves. Radiowaves yana iya tafiyar nisan mita miliyan dari uku a duk second daya (300, 000, 000m/s) daidai da gudun kilomita dubu dari uku a duk second daya (300, 000km/s). Inde kana da na’urar GPS a wajen ka, wato GPS receiver duk inda kake a doron kasa ana iya gano ka.

Kuna iya karanta bayanin mu daya gabata mai taken MENENE SATTILETE ⤵⤵⤵
➡ Dandalin kimiyya : Sadarwar Satellite. 

Rubutawa
Nura Mahdi Idris

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you