Connect with us
Ramadan KAREEM

Dandalin Kimiyya

Dandalin kimiyya : Menene Gravity ?

Published

on

Menene Gravity?

Sau dayawa dalibai da sauran mutane da suke karatu a bangaren kimiya da fasaha wasu basa gane menene gravity. Wasu ma cewa suke babu wani abu wai shi gravity. Saboda gravity ba abu bane da ake iya gani da ido sai dai aji shi ajiki. Kai ina iya cewa ajikin ma bakowa bane zai gane cewa gravity yana shafar shi.

Dandalin kimiyya : Menene Gravity ?, Gravity Force
Gravity Force

Kafin mufara bayanin menene gravity, yakamata mu fahinci menene Force da kuma Field a physics, acikin wani post danayi abaya nayi bayanin menene force – idan kanason kasan menene force sai kaje wajen searching a Facebook ka rubuta ‘Menene Force?’ zakaga bayanin insha Allahu. Amma ganan bayanin force da field a takaice.

Menene Force?

Idan akace force a turance ana nufin tursasawa, ko sa karfi domin yin aiki – kaman turawa(push), ko dagawa(lift), ko dannewa(compress), ko jawowa(pull). Wani lokacin kuma ana nufin adadin karfin kanshi. To force de karfi ne da ake sawa domin jawo wani abu, ko tura wani abu.

DUBA KUMA : Dandalin kimiyya : Menene Energy?

Asani Force da Energy ma’anarsu ba daya bane – sai dai da Hausa dukkansu muna fassarasu amatsayin karfi. Kwanakin baya na fara bayanin menene energy da ire irensa. Idan kanaso kasamu wancan post din, kawai ka shiga wajen searching na Facebook ka rubuta ‘Menene Energy?’ kayi Ok. Zaka sameshi insha Allahu.

Menene Field?

A turance idan akace field ana nufin fili, ko kuma wani yanki da yake da fili. To a physics idan akace field ana nufin fili ko waje da sai irin wannan abun kadai yakejin karfin jawowa ko korewa(force of attraction or repulsion) daga dan uwanshi ba tare da anga alamar wani daga cikinsu yasa hannu ko wani abu yajawo dan uwansa ba. Nasan ba’a gane abun da nake nufi anan ba, amma idan nayi misali insha Allahu za’a gane me nake nufi.

Misali kasamo maganadisu(magnet), kasamo roba da kwali da karfe. Idan ka ajiye kwali ko robar a kusa da maganadisun zakaga cewa maganadisun bazai jawo su ba, kuma bazai kama su ba. Amma kana kawo karfe kusa da maganadisun nan take zakaga maganadisun yajawo wannan karfe. Saboda roba da kwali ba field nasu bane shiyasa maganadisun bai jawosu ba.

Abun da nakeso a fahinta anan shine shin lokaci da maganadisun yake jawo wannan karfen ana ganin wani abu kaman hannu a tsakanin maganadisun da karfen?

Amsa itace ba’a ganin komai kawai sai dai aga maganadisun yakama karfen. Wannan shi ake kira magnetic field(wato field din maganadisu). Magnetic field yana daya daga cikin manya manya ire ren force guda biyu a physics(contact and uncontact force). Abun lura maganadinsun yasa karfin jawowa(force of attraction) yajawo karfen. Amma ba’a ganin da menene maganadisun yake jawo karafa.

DUBA KUMA : Dandalin kimiyya : Menene Energy?

Kada a manta ba bayanin magnetic field mukeyi ba, muna bayanine akan menene gravity. Kamar yadda maganadisu yakesa karfi yajawo ko kore karfe haka shima gravity yake jawo duk abun dayake Da nauyi zuwa kasa.

Gravity, field force ne, wato wani irin karfi ne da yake jawo kowane abu mai nauyi(mass) zuwa kasa. Zaka gane haka idan kajefa dutse yayi sama. Yayin da kajefa dutse yayi sama – zakaga yayi can sama bayan wani lokaci zai fado kasa. Idan da ace babu karfin gravity da sai dai wannan dutsen yayi ta tafiya sama bazai fado kasa ba sai illa masha Allah.

Gravity ikon Allah ne, dayake jawo duk wani abu mai nauyi zuwa kasa. Gravity yana kama tsakiyan abu(centre of mass) ne. A dai dai kusurwa ta digiri casa’in(90º angle).

Gravity shi yake sa duk wani abu dayake cikin sarari(space) yakasance celestial. Idan akace celestial ana nufin duk wani abun dayake cikin sarari yake kewaye wata duniya(planet) ko wani star. Misalin celestial sune planet, asteroid, satellite da sauransu.

Nasan mafi yawa ansan menene planet da satellite, watakila wani zaice menene asteroid din nan?

Asteroid dai wani abu ne karami kaman dutse acikin sarari dayake kewaye wata planet ko star. Asteroid karami ne idan aka kwatanta girmansa da girman planet. Amma asteroid ba karami bane, asteroid yana da girman gaske domin girmansa zai kai girman wani birni ko gari acikin wannan duniyar.

Gravity shi yake rike da duniyoyi(planets) da taurari(stars) da gas da kura(dust) a cikin galaxy.

Lokacin da jirgin sama zai tashi sama nau’in karfi guda hudu ne suke aiki akanshi kuma dolene asamu daidaito(balanced force) atsakanin su. Wadannan forces din sune gravity, da thrust, da air resistance, da kuma lift.

Gravity munce karfi ne da yake jawo abu zuwa kasa, to anan ma shi yake jawo jirgi zuwa kasa.

Lift shi kuma shine karfin dayake sa jirgin yatashi sama. Wannan karfin ana samun shi ne ta hanyar wasu abubuwa da ake kira flap da airfoil da suke jikin fiffiken(wings) jirgi. Dolene karfin gravity da lift su zama daya ko kuma lift yafi gravity. Amma idan gravity yafi karfin lift jirgin yana iya fadowa.

Air resistance shima karfine dayake kalubalantar gudun jirgi yayin dayake tafiya asararin samaniya. Shiyasa aka tsara gaban jirgi yayi tsini.

Thrust shine karfin dayake zuwa daga injin jirgin, kuma shine karfin dake sa jirgin yayi tafiya yayin da jirgin zai tashi. Bayan yatashi kuma jet da suke jikin fiffiken jirgin su suke sashi yayi tafiya acikin iska. Anan dole thrust yafi air resistance. Domin idan air resistance yafi thrust jirgin zai descend wato yakasa tafiya daga karshe sai de yafado.

DUBA KUMA : Dandalin kimiyya : Menene Energy?

Karfi hudu nan dolene su zama dai dai, ko kuma akalla biyun suzama sun dan fi biyun, wato lift da thrust su zama sun dan fi gravity da air resistance.

Karfin gravity ya banbanta daga wata duniyar zuwa wata. Misali karfin gravity na Earth shine 9.8N/kg, to karfin gravity na duniyar Mars shine 3.7N/kg, Wata(Moon) kuma 1.6N/kg, na Rana(Sun) kuma 274N/kg a takaice.

Bari mu tsaya anan sai kuma munzo dawani post akan wani abun kuma. Kuna iya rarrabawa ko turawa abokanku domin suma su karanta su amfana. Ahuta lafiya.

RUBUTAWA
Dalibin Physics
Nura Mahdi Idris

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Copyright © 2012 Present | Powered by AREWASOUND LTD.