Connect with us
Ramadan KAREEM

bincike

Dandalin kimiyya : Menene solar system

Published

on

Dandalin kimiyya : Menene solar system

Idan akace solar system ana nufin Rana (Sun) da sauran duniyoyi (planets) da suke kewayeta a ko yaushe. Wadannan duniyoyin sune Mecury, da Venus, da Earth, da Mars, sai Jupiter, da Saturn, da Uranus, da kuma Neptune. Watakila wani zai ce meyasa, bansa Pluto ba?

Pluto itama planet ce amma ba kaman sauran planet din ba. Idan akace planet to anaso asamu wata planet din a kusa da ita wanda suke da yanayi kusan iri daya. Misali, duniyar da muke ciki wato Earth tana da yanayi kusan iri daya da duniyar Mars. Yanayin shine suna da kasa mai tauri, kuma suna kusa da juna, sannan akwai ruwa. Ita kuma pluto babu wata planet mai irin yanayin ta acikin planet takwas din nan da suke solar system. Sannan ita pluto karama ce batakaisu girma ba, shiyasa ake ce mata dwarf planet.

Dandalin kimiyya : Menene solar system

Duniyoyin nan guda takwas da suke a solar system an rabasu gida biyu. Na farko su ake cewa Terrestial, sai kuma na biyun sune Jovian.

DUBA KUMA : Dandalin Fasaha : Yadda Ake Hada Software ; Gabatarwa

Terrestrial:
Sune su Mecury, da Venus, da Earth da kuma Mars. Wadannan planet guda hudu suna da yanayi kusan kala daya. Gaba dayansu basu da girma, idan aka kwatanta girmansu da duniyoyin da suke Jovian. Suna da doron kasa mai tauri kaman dutsi. Wasun su basu da wata (moon), wasu suna da wata, amma mara yawa (bawai su January da February ko March ake nufi ba) ana nufin wata wanda idan dare yayi zakaga yana haska duniya.

Jovian:
Su Jupiter, da Saturn, da Neptune, da Uranus sune jovian planet. Su kansu an rabasu gida biyu da Gas giants, da kuma Ice giants.

Gas giants sune Jupiter, da Saturn. Ice giants kuma sune Neptune, da Uranus.

Gas giants ana samun sinadarai na iskar Helium, da Hydrogen. Ice giants kuma ana samun duwatsu, da kankara, da ruwa mai dauke da sinadarai daban daban, da sinadarin ammonia, da kuma methane (wanda ake amfani dashi a injina).

Gaba daya duniyoyin jovian guda hudu suna da wata moon masu yawa. Kuma ba su da kasa mai tauri. Sannan suna da girma sosai idan aka kwatanta girmansu da duniyoyin terrestrial.

Duniyar Mecury itace tafi kusa da rana. Kuma tana orbit mara tsawo, wato kasa da kwanaki dari shine shekara daya acan. Venus itace duniyar da tafi kowace duniya zafi, saboda akwai sinadarin iskar carbondioxide a doron kasarta. Kuma akwai zubar narkakken dutse mai yawa a doron kasar wancan duniyar. Sannan zafi yakai maki dari takwas da sittin da bawai a ma’aunin zafi na Fahrenheit (867ºF), wato dai dai da maki dari hudu da sittin da hudu a ma’aunin zafi na Celsius (436ºC).

Earth itace duniya da dan Adam da dabbobi zasu iya rayuwa acikinta. Saboda tsarin ruwa da Allah yayi mata, zaisa halittu su rayu. Mars itace duniyar terrestrial ta karshe, tana da yanayin doron kasa mai ruwa ruwa ko kankara.

Dandalin kimiyya : Menene solar system

Duniyoyin Jovian, Jupiter itace duniya mafi girma acikin solar system. Daga ita sai duniyar Saturn. Neptune itace duniya ta karshe a solar system wajen nisa. Tsakanin ta da rana akwai nisan kilomita biliyan hudu da rabi (4.5billion kilometres) dai dai da nisan miles biliyon biyu da digo takwas (2.8billion miles). Neptune itace duniyar da tafi kowace duniya sanyi, saboda tafi kowace duniya tazara zuwa rana. Sanyin dake wannan duniyar baikai ko da maki daya ba.

Bayan duniyoyi akwai iska da giza gizai da wasu abubuwa masu kama da duwatsu da ake samu suma suna kewaye rana kamansu ceres da asteroid da makamantansu. Wani zai iya cewa meyasa Venus tafi Mecury zafi, alhali Mecury tafi kusa da rana akan Venus?

Yanayin sararin samaniyar Mecury akwai wasu sinadarai da suke rage karfin haske da zafin rana zuwa cikinta. Yayin da sinadaran da suke saman Venus basu kai na Mecury karfi ba. Shiyasa Venus tafi Mecury zafi

DUBA KUMA : Dandalin Fasaha : Yadda Ake Hada Software ; Gabatarwa

Duniyar da muke ciki Earth akwai sinadarin iskar ozone (ozone layer) wanda yake sama damu a nisan kilomita ashirin da biyar (25 kilometres). Shine yake rage karfi da zafin hasken rana kafin ya karaso doron kasa.

ma’aunin zafi na Fahrenheit (867ºF), wato dai dai da maki dari hudu da sittin da hudu a ma’aunin celcious.

Rubutawa
Nura Mahdi Idris

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Copyright © 2012 Present | Powered by AREWASOUND LTD.