Dandalin KimiyyaDandalin kimiyya : Nisan Dake Tsakanin Duniya Da Wata.

Dandalin kimiyya : Nisan Dake Tsakanin Duniya Da Wata.

-

Dandalin kimiyya : Nisan Dake Tsakanin Duniya Da Wata.

Yaya Nisan Dake Tsakanin Duniya Da Wata Yake?

Wasu daga cikin mutane suna tunanin cewa wata da suke gani a sama da dare yana haska cikin duniya, wai shima a cikin duniyar yake – amma ba haka bane. Za ka fahimci cewa wata da kake gani a sama da dare ba a cikin duniya yake ba, idan ka duba rubutun da nayi kwanan baya mai taken Menene Satellite?đŸ”—

Duniyar nan da muke cikin ta wato Earth da Moon wato wata dukkan su muna iya cewa duniyoyi ne da suke da yanayi kusan iri daya. Amma kasancewar wata dan karami ne sosai idan aka kwatanta girman sa da girman duniya, yasa wata satellite ne ba planet ba.

DUBA KUMA : Dandalin kimiyya :  Bayani akan International Space Station

Abun da yasa aka ce wata shima duniya ce, saboda yana da yanayi irin na duniyan nan. Doron kasa na wannan duniyar dana wata duk kusan iri daya ne. Sai dai a cikin wata akwai sinadaran iska masu illa ga lafiyar dan Adam ko dabba. Tsakanin doron kasa na duniyar nan zuwa wata akwai gurare a sama da ake kira Exoshpere, da Troposphere, da Thermosphere da sauran su. Wadannan guraren zamuyi bayanin su a takaice idan Allah yaso.

Atmosphere
Atmosphere yana nufin doron kasa, ko kuma iskar gas din da ta kewaye duniyan nan wato Earth, ko kuma wata duniyar kaman su Mars, da Saturn, da sauran su. Atmosphere itace muke takawa lokacin da muke tafiya, da gina gidaje, da hanyoyi, da kasuwanni, da sauran su duk a kanta.

Troposphere
Troposphere yana sama a nisan kilomita sha daya (11km) tsakanin sa da doron kasa, wato daidai nisan miles bakwai (7miles). Yanzu sama da shekaru dari kenan da kirkiro jirgin sama, wanda ya kawo sauki da canji ga harkokin tafiye tafiyen dan Adam da sauran kayaiyakin sa na rayuwar yau da kullum. Jirgin sama na kasuwanci ko na zirga zirgan mutane idan ya tashi sama yana tafiya ne a daidai nisan da ake kira Troposphere. Haka kuma daidai tsayin tsaunin nan mai taken Mount everest.

Stratosphere
Stratosphere yana sama daga nisan kilomita sha daya zuwa hamsin (11-50km) wato daidai daga miles bakwai zuwa talatin da daya (7-31miles). A daidai wannan nisan ana samun jiragen sojoji, da jirgi mara matuki na leken asiri, da balan balan na auna yanayi, da kuma mutane masu yin nitso daga cikin sararin samaniya zuwa doron kasa, wadanda ake cewa Sky divers, ko Higest sky divers a turance.

Mesosphere

Mesosphere yana can sama daga nisan kilomita hamsin zuwa tamanin (50-80km) wato daidai nisan miles talatin da daya zuwa hamsin (31-50miles). A daidai tsakanin nisan da ake kira mesosphere rocket yake tsayawa ya fado. Sai kuma satellite din rocket din ya dakko, ya cigaba da tafiya shi kadai har sai yakai nisan da ake bukata, sannan zai bude kansa – sai ya fara zagaye duniya.

Thermosphere
Thermosphere kuma yana nan a nisan kilomita tamanin zuwa dari bakwai (80-700km) wato daidai da nisan miles hamsin zuwa dari hudu da arba’in (50-440miles). Thermosphere ana samun satellite a wajen, sannan kuma akwai tsananin zafi. Kalmar thermo tana nufin zafi, ko kuma abu mai zafi. Ana samun satellite anan har International Space Station anan take zagaye duniya. Saboda tana a nisan kilomita dari hudu (400km) tsakanin ta da doron kasa.

DUBA KUMA : Dandalin kimiyya : Bayani akan International Space Station

Exosphere
Exosphere yana daga nisan kilomita dari bakwai zuwa kilomita dubu goma (700-10,000km) wato mile dari hudu da arba’in zuwa dubu shida da dari biyu (440-6200miles). A nisan da ake kira Exosphere kuma babu komai, kawai fili ne wato vaccum space. Sai kuma iska mai karfi dake wajen. Anan nisan ma ana samun satellite masu yawa.

Moon To Earth
Daga duniyan nan wato Earth zuwa duniyar wata wato Moon akwai nisan kilomita dubu dari uku da tamanin da hudu da dari hudu (384400km) wato daidai da nisan miles dubu dari biyu da talatin da takwas da dari tara (238900miles). Sannan haske da kake gani na wata daga rana yake zuwa masa, sai ya juyo hasken (reflect) zuwa duniyan nan.

Rubutawa
Nura Mahdi Idris

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you