Dandalin KimiyyaDandalin kimiyya : Yadda Drone Yake Aiki

Dandalin kimiyya : Yadda Drone Yake Aiki

-

 Dandalin kimiyya : Yadda Drone Yake Aiki

Yadda Drone Yake Aiki

Drone jirgine mara matuki wanda ake amfani da shi domin leken asiri, ko tattara bayanan sirri, ko kuma kai hari. Drone dai kala biyune akwai babba, kuma akwai karami. Za mu yi bayanine akan kimiyyar physics din karamin drone wanda ake kira quadcopter.

Quadcopter ko kuma drone wani dan karamin jirgine wanda a yau ake amfani da shi wajen daukan hoto da kuma hoton bidiyo. Drone ana tukashi da remote, idan ka na tukashi za ka ga kaman ka na yin game ne.

DUBA KUMA : Dandalin kimiyya : Menene Optical Fibre Cable ?

Drone ya na samun wutar lantarki daga batirin (battery) jikinsa, kuma batir dinsa kaman batir din waya ya ke – wato shima Lithium ion battery ne ba Lead acid battery ba. Lead acid battery ko lead accumulate battery shine batir din mota da mashin.

Jikin quadcopter akwai kafafuwa guda hudu, kuma kowace kafa jikinta akwai moto mai dauke da farfela (propeller) juyawan da wadannan farfelolin su ke yi shine ya ke sawa drone din ya tashi sama. Kowace farfela duk minti daya tana juyawa ko wainawa (revolution) sau dubu ashirin da takwas da dari biyar duk minti daya (28, 500RPM), wato juyawa sau dari hudu da saba’in da biyar duk second daya (475RPS). Hakan shi zai sa drone ya tashi sama sosai.

Moto guda hudu da su ke jikin kafafuwan quadcopter biyu su na juyawa daga hagu zuwa dama (clockwise), sannan biyu ‘yan uwansu su kuma su na juyawa daga dama zuwa hagu (anticlockwise). Wannan juyawar da su ke yi clockwise da anticlockwise ya sa quadcopter idan ya tashi sama zai iya tafiya ta kowane bangare. Haka kuma zai iya yin kwana a duk lokacin da aka ba shi umarni ta hanyar remote din da ake sarrafa shi.

Duba kuma : Dandalin kimiyya : Menene 5G? (Gabatarwa)

Quadcopter ya na amfani da GPS ta yanda za a iya ganosa koda ya bace indai yana aiki – amma idan batirinsa ya yi sanyi ganosa zai yi wahala, sai dai a gano inda ya ke daga karshe kafin batirinsa ya mutu. Sannan ya na amfani da radiowaves domin sadarwa tsakaninsa da GPS satellite wadanda su ke can cikin sararin samaniya.


“Shi drone yawanci kananun sa suna amfani ne da RF waves. RF yana nufin radio frequency, Rf wave yakasu kashi biyu, wasu suna amfani da FM ( frequency modulation) wave wasu kuma AM (amplitude modulation) wave. manya manyan drone Wanda suke cin nisan zango domin leken asiri suna amfani da gps (global positioning system).

Remote din shine Transmitter din Sannan a ajikin drone din akwai radio receiver din.

Shi drone yana iya fahimtar umarnin da remote din yabashine
Ta hanyar frequency, ajikin receiver din drone din akwai circuit din da ake kiransa da suna frequency to voltage converter. Domin shi remote din yana tura frequency ne ma jirgin while shi kuma receiver din yana converting dinsa as a voltage command.”

Kamaluddeen Kmc Encyclopedia

Idan moto din jikinsa su na juyawa da sauri za ka ga ya yi can sama, wato idan yanada caji ya na tashi sama sosai, akasin haka kuma idan batirinsa ya fara sanyi zai yi kasa kasa. Idan quadcopter ya na tafiya ta gabas kai kuma ka na so ya yi kwana ya dawo ta yamma ko kudu ko arewa kawai a remote za ka juya wadannan scroller ko analogue din masu kama da na hannun game din Play Station (PS) – a nan take zai yi kwana.

Yanda fasahar ta ke aiki shine moto din da su ke bangaren da kake so quadcoptern ya bi, su za a karawa gudu. Misali, lokacin da quadcopter ya ke tafiya ta gabar kowace moto ta na samun wuta mai karfin voltage biyar (5volts), sannan dukkansu su na juyawa sau dubu ashirin duk minti daya (20, 000RPM). Idan aka karawa biyu karfin wutar daga biyar zuwa bakwai (7volts) sai gudun juyawarsu ya karu daga dubu ashirin duk minti daya zuwa dubu talatin duk minti daya (30, 000RPM). Kenan bangaren da gudunsa ya karu shi zai rinjayi daya bangaren.

Amma fa wannan abun duk ya na faruwane a cikin remote din da ake sarrafa quadcopter. Jikin quadcopter akwai camera wanda ta ke daukar bidiyo. Lokacin da quadcopter ya ke aiki moto guda hudu na jikinsa gudunsu daidaine. Amma idan moto guda daya gudunta ya fi gudun sauran ukun – to quardcopter zai fara tafiya ta bangaren da ya fi juyawa da sauri.

DUBA KUMA : Dandalin kimiyya : Menene Optical Fibre Cable ?

Yanda jirgin ya ke tashi sama shine farfelolinsa su na danne iska zuwa kasa ita kuma iskar ta na tura farfelolin jirgin sama. Daman farfelolin an yi su a karkace, su ba a tsaye su ke ba, kuma su ba a kwance su ke ba. An karkatasu daidai wani angle wanda ake cewa angle of attack.

Rubutawa
NURA MAHDI IDRIS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you