Connect with us
Ramadan KAREEM

Dandalin Kimiyya

Dandalin Kimiyya : Yadda Girman Memory Na Computer Yake

Published

on

Dandalin Kimiyya : Yadda Girman Memory Na Computer Yake.

Yaya Girman Memorin Computer Yake?

Computer tana ajiye bayanai ko wani file akan ta a matsayin binary. Bidiyo ko hoto ko application da muke ajiyewa akan wayoyin mu da computer suna zama ne a matsayin 0 da 1. Sannan akwai ma’ajiyi na computer kala kala, ko kuma ace girma girma, wannan yafi wancan daukan abubuwa.

Dandalin Kimiyya : Yadda Girman Memory Na Computer Yake

Akwai ma’ajiyi (Memory) iri daban daban na computer da waya, wadanda muke amfani dasu a bangarori dadama. Da ikon Allah zanyi bayanin wadannan ma’ajiyan da kuma girman su.

DUBA KUMA : Dandalin Fasaha : Yadda Ake Hada Software ; Gabatarwa

Bit yana iya daukan abu guda biyu ne kadai, a matsayin true or false, ko yes or no, ko on and off, amma dai amfani da 1 da 0. Bit guda takwas sune suke zama byte daya. Shi kuma byte daya yana daukan abubuwa guda dari biyu da hamsin da shida. Bawai bidiyo ko hoto ko waka dari biyu da hamsin da shida nake nufi ba, wasu kananun abubuwa ne da nauyin su baikai harafi daya ba.

Nasan wani zaiyi mamakin cewa bit yana daukan abu biyu ne kadai, kuma bit takwas sune byte daya. Amma kuma daya byte yana daukan abubuwa dari biyu da hamsin da shida. Alhali kuma idan aka ce biyu sau takwas, amsar ita ce sha shida, ba dari biyu da hamsin da shida ba.

Yanda abun yake shine zaka lissafa biyu sau biyu abun da ya baka shima sau biyu har sai kayi haka sau takwas. Ga yanda akeyi biyu sau biyu hudu kenan. Hudu sau biyu takwas. Takwas sau biyu sha shida. Sha shida sau biyu talatin da biyu. Talatin da biyu sau biyu sittin da hudu. Sittin da hudu sau biyu yazama dari da ashirin da takwas. Dari da ashirin da takwas sau biyu yakama dari biyu da hamsin da shida.

DUBA KUMA : Dandalin Fasaha : Yadda Ake Hada Software ; Gabatarwa

Byte yana iya daukan lamba, ko harafi, ko launi. Idan kakara adadin byte zai dauki lambobi, jimlolin rubutu, da sauransu. Byte guda dubu daya da ashirin da hudu shine kilobyte daya.

Matsakaicin hoto mai kyau yana kai nauyin kilobyte dari (100kB) ko sama da haka. Kilobyte guda dubu daya da ashirin da hudu shine megabyte. Mega kuma yana nufin miliyon, wato akwai byte miliyon daya da wani abu a cikin megabyte daya kenan.

Audio mai tsawon minti daya yana iya kai megabyte daya (1MB). Floppy disk mai tsawon inchi uku da rabi (3.5 inch) yana kai girman megabyte daya da digo arba’in da hudu (1.44MB).

Faifayin CD na bidiyo CD yana kai girman megabyte dari bakwai (700MB). Gigabyte yana daukan megabyte dubu daya da ashirin da hudu (1024MB).

Faifayin CD na bidiyon DVD yana daukan gigabyte hudu da digo bakwai (4.7GB). Faifayin DVD na Blue ray disc yana daukan gigabyte ashirin da biyar (25GB). Flash drive yana daukan gigabyte talatin da biyu (32GB), akwai mai gigabyte sittin da hudu (64GB) da kuma gigabyte dari da ashirin da takwas (128GB).

Terabyte yana daukan gigabyte dubu daya da ashirin da hudu (1024GB). Hard drive yana daukan daga terabyte daya zuwa terabyte takwas (1-8TB)

Petabyte yana daukan terabyte dubu daya da ashirin da hudu (1024TB). Kamfanonin da suke samar da hosting ga mutane a internet, da su YouTube, da Facebook, da Amazon duk suna amfani da ma’ajiyi mai daukan terabyte dubu daya da ashirin da hudu (1024TB).

Exabyte yana daukan petabyte dubu daya da ashirin da hudu (1024PB). Gaba daya traffic na internet a duniya na wata daya ana aunashi da Exabyte, wato petabyte dubu da ashirin da hudu (1024PB).

DUBA KUMA : Dandalin Fasaha : Yadda Ake Hada Software ; Gabatarwa

Sai kuma Zettabyte wanda duk guda daya yana daidai da exabyte dubu daya da ashirin da hudu (1024EB). Daga karshe kuma sai Yottabyte(1024ZB). Wadannan biyun na karshe haryanzu bansan kuma a ina ake ai dasu ba. Sai dai ayi hakuri da kuskuren da watakila za’a samu a rubutun nan.

Rubutawa
Nura Mahdi Idris

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Copyright © 2012 Present | Powered by AREWASOUND LTD.