Dandalin KimiyyaDandalin Kimiyya : Yadda Optical fingerprint scanner ta ke...

Dandalin Kimiyya : Yadda Optical fingerprint scanner ta ke aiki

-

Dandalin kimiyya : Yadda Optical fingerprint scanner ta ke aiki

– Menene optical fingerprit scanner
– Yaya Optical fingerprint scanner take
– Yadda optical fingerprint scanner ke aiki

Kuna a Shafin Arewasound.com ne
Mungode

Optical fingerprint scanner daya ce daga cikin tsarin tsaron na’ura wanda ake amfani da ita a zamanin yau. Ana amfani da optical fingerprint a bankuna, da wajen rajistar layin waya, da makarantu, da kuma bangaren tsaro ko da ya ke nan ne ma amfani da fingerprint ya samo asali. Akwai hanyoyin tsaron na’ura guda uku wadanda su ke amfani da biometrics domin tantance mutum.

Duba kuma : Dandalin kimiyya : Menene 5G? (Gabatarwa)

Biometrics shine amfani da wani sashe na mutum domin tabbatar da cewa shi ne mai wannan bayanan. A yau akwai tsarukan tsaron na’ura guda uku wadanda su ke tantance mutum ta hanyar biometrics na shi. Akwai wanda ake amfani da fuska (facial recognition), akwai wanda ake amfani da kwayar ido (iris), da kuma wanda ake amfani da tambarin dan yatsa (thumb).

Kowane mutum, biometric na shi daban ne da na wani, ko da mutum Hassan da Hussaini ne, to biometrics na su daban ne. Sannan kuma hatta idon mutum na bangaren hagu da na dama akwai banbanci. Haka ma zanen dan yatsa kowane mutum na shi daban ne.

To bari mu dawo bayanin yanda fasahar tantance mutum ta hanyar dan yatsa ta ke aiki. Optical fingerprint aikinsa gaba daya ya dogara ne akan haske wanda ido ya ke iya gani (visible light), ko kuma infrared light (wato hasken da ido ba ya iya gani). Optical fingerprint ya na da bangarori guda uku.
1- Na farko shine light source ko kuma laser,

2- Na biyu kuma shine prism glass wato glashi mai kusurwa uku,

3- Na Uku shine sensor.

Light source ko sensor shine ya ke samar da haske a cikin optical fingerprint, kuma cikinsa akwai dan karamin koyin wuta (LED). Wannan dan karamin koyin wutan ya na bayar da jan haske (red spectrum) ko kuma infrared (wanda shi din ma jan haske ne wanda idon mutum ba ya iya ganinsa).

Lokacin da mutum ya daura hannunsa akan optical fingerprint bayan lokaci kadan laser za ta saki jan haske ya yi sama ya shiga ta cikin prism glass ya wuce (refraction). Yayin da hasken ya shiga cikin prism din zai wuce wasu daga cikin kwayoyin hasken za su fita daga cikin prism din zuwa hannun mutum.

DUBA WANNAN : Dandalin Fasaha : Yadda Ake Hada Software ; Gabatarwa

Yayin da wadannan kwayoyin hasken su ka karaso wajen dan yatsar mutum, wasu daga cikinsu za su daki dan yatsar mutum su koma kasa (reflection), wasu kuma hannun mutum zai shanyesu (absorption). Misali, idan laser ta saki kwayoyin haske (photons) guda biliyan goma to lokacin reflection da absorption adadin kwayoyin hasken da za su karaso sensor zai rage. Watakila kwayoyin haske guda biliyan shida da rabi su dawo, ya yin da aka rasa biliyan uku da rabi wajen reflection, da reflection, da kuma absorption.

To kwayoyin hasken da su ka rage, wato wadanda su ka daki dan yatsar mutum su ka dawo kasa kowane daga cikinsu daman ya na dauke da wata siffa daga bangaren da ya taba a jikin tambarin yatsar mutum. Sannan su na zuwa wajen sensor shima sensor zai shanyesu gaba daya, sai ya canzasu zuwa hoto (amma hoton tambarin dan yatsa) daga nan sai ya matse hoton (compress) sannan ya canza wannan hoton zuwa binary code, sai waya ko computer ko wannan na’urar ta ajiye wannan bayani akanta.

Optical fingerprint scanner haka ta ke aiki a takaice, kuma hakan ya na faruwa cikin kankanin lokaci. Amma duba da karancin aikin optical fingerprint kaman lokacin da hannun mutum ya ke da datti, da kuma lokacin hannunsa ya ke wanke bayanin tambarin dan yatsarsa zai iya canzawa a optical fingerprint wannan ya sa a yanzu wayoyi da computer su ka koma aiki da fasahar capacitive fingerprint, da kuma ultrasonic fingerprint wanda aka fara amfani da ita a 2018.

DUBA KUMA : Dandalin kimiyya : Menene Optical Fibre Cable ?

Ita kuma capacitive fingerprint scanner ta na aikine da cajin (charge) da ya ke jikin hannun mutum, kaman yanda touchscreen din wayar Android ko iPhone ya ke aiki da wata fasaha da ta ke aiki da resistance ko capacitance na hannu ko wani bangare na jikin mutum. Wato dai a takaice shima jikin mutum ya na ajiye cajin wutar lantarki kaman yanda capacitor ya ke yi. Sai dai wutar da hannun mutum ya ke ajiyewa ba ta da karfi kuma ba ta da yawa.

Duba kuma : Dandalin kimiyya : Menene 5G? (Gabatarwa)

Daga karshe kuma ina addu’ar Allah ya ji kan abokinmu, abokin karatuna da bincike Yusuf Salisu Blogging, domin ya taimaka mun wajen fassara tare da tattara bayanai akan Fingerprint scanner.

Bincike da rubutawa:
– Yusuf Salisu Blogging
– Nura Mahdi Idris

Publishing on Arewasound by :
– Abdullahi Hashim Abdullahi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you