Smart News EverydayAREWASOUND
سُبحَانَ اللّهِ وَ بِحَمْدِهِ ، سُبحَانَ اللّهِ الْعَظِيمِ

Labarai Donald Trump ya fice daga White house a matsayin...

Donald Trump ya fice daga White house a matsayin shugaban kasar Amurka

-

SPONSORED LINK

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da jawabinsa na bankwana, wanda a ciki yake cewa: “Mun yi abin da ya kawo mu – har ma da kari.”

A wani sakon bidiyo da aka wallafa a YouTube, shugaban ya ce ya “sauke nauyin da aka dora mana, wanda shi ne dalilin da ya sa kuka zabe ni.”

Sai dai har yanzu Mista Trump bai amince da shan kaye a zaben watan Nuwamba ba, zaben da Joe Biden na jam’iyyar Democrat ya lashe.

Za a rantsar da Joe Biden matsayin shugaban Amurka na 46 ranar Laraba.

Makonni biyu na karshen mulkin Mista Trump sun kasasnce cike da takaddama bayan wani hari da mabiyansa suka kai ginin majalisar dokokin kasar, inda suka ce suna son sauya sakamakon zaben shugaban kasar saboda gwaninsu ya sha kaye.

“Hari irin wannan yana da mummunan tasiri kan dukkan abubuwan da mu Amurkawa ke alfahari da shi ne. Ba za a taba amincewa da shi ba,” in ji Trump.

Sai dai bai ambaci sunan wanda zai gaje shi ba, duk da cewa ya nuna karshen mulkinsa ya zo.

“Mun dauko aikin mayar da martabar Amurka ga dukkan Amurkawa. Yayin da nake kammala wa’adina a matsayin shugaban Amurka na 45, ga ni tsaye gare ku ina alfahari da abubuwan da muka cimma tare.”

Karanta Wannan:-  Communal Clashes: Enugu govt imposes curfew on Oruku Community

Ya kara da cewa: “Mun cimma dukkan abubuwan da muka sa a gaba har ma da wasu na daban.”

“Yayin da kuma a wannan makon za mu kaddamar da sabuwar gwamnati, muna son a yi ma ta addu’a domin Amurka ta kasance cikin zaman lafiya da karuwar arziki. Muna kuma mika fatan mu na alheri a gare su,” a cewar Mista Trump.

Karanta Wannan:-  Communal Clashes: Enugu govt imposes curfew on Oruku Community

Ya kuma soki masu amfani da tashin hankali wajen cimma muradai na siyasa.

A cewarsa: “Dukkan Amurkawa ba su ji dadin harin da aka kai wa ginin majalisar kasarmu ba.”

Ya kuma ce rike mukamin shugaban Amurka abin alfahari ne da ba ya misaltuwa.

“Ina mika godiya ta ga wannan abin alfaharin, wanda haka na dauke shi, babban abin alfahari,” a cewarsa.

Ya bukaci da kada su manta cewa duk da cewa a “matsayinmu na Amurkawa, za mu rika samun bambance-bambance, amma kasarmu kasa ce ta mutane masu kwazo da mutunci da biyayya da kuma masu son zaman lafiya, wadanda ke son kasarmu ta bunkasa, ta kuma zama mai nasarori. Lallai mun kasance kasa abar alfahari.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

CHECK OUT
How to Setup Glo Unlimited Browsing 2021

Airtel Bonus Code You Can’t Miss 2021

Read more at SOURCE: This post (Donald Trump ya fice daga White house a matsayin shugaban kasar Amurka) firstly published at hutudole.com on 2021-01-20 17:05:16

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you