Connect with us
Ramadan KAREEM

Labarai

Fasa Gidan Yari: Yadda wasu kauyawa suka kona wani Fursuna da ya dawo gida

Published

on

Fasa Gidan Yari: Yadda wasu kauyawa suka kona wani Fursuna da ya dawo gida

Wasu fusatattun mazauna kauyen Umuawom dake yankin Ihodimeze, a karamar hukumar Ikeduru a jihar Imo a ranar Laraba sun cinnawa wani fursuna wuta wanda ya dawo gida daga Cibiyar Gyara da ke Owerri wanda aka kai wa hari a ranar Litinin.

An bayyana cewa, fursunon da ya gudu, wanda ba a iya tantance asalinsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto, an ce ya fito ne daga yankin Ogwa da ke kusa da karamar hukumar Mbaitoli ta jihar Imo amma ya girma ne a ƙauyen Umuawom, wanda nan ne mahaifiyarsa.

Ya kuma shiga harkar satar mutane wanda ya shafi daya daga cikin iyalan kauyen Umuawom amma daga baya aka kama shi aka kuma tsare shi har tsawon shekara guda.

Koyaya, lokacin da ya tsere daga Cibiyar Gyara a ranar Litinin, an ce ya tafi kai tsaye zuwa ɗaya daga cikin dangin da suka ba da shaida a kansa kuma ya yi masu barazanar kisa.

Ance ya yi kokarin hallaka wani daga cikin dangin da ke kauyen Umuawom da bindiga.

Majiyoyin Kauyen sun shaidawa manema labarai cewa wannan yunkurin da yayi, ya sanya mazauna garin daukar doka a hannun su, kuma nan take suka cinna masa wuta.

Kakakin rundunar ‘yan sanda, Orlando Ikeokwu, ya ce ya samu labarin faruwar lamarin amma ba zai iya tabbatar da hakan a hukumance ba, har sai jami’an sun gama hada bayanai.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


CHECK OUT
[related_posts_by_tax]
How to Setup Glo Unlimited Browsing 2021

Airtel Bonus Code You Can’t Miss 2021

SOURCE: This post (Fasa Gidan Yari: Yadda wasu kauyawa suka kona wani Fursuna da ya dawo gida) firstly published at www.hutudole.com on 2021-04-08 07:00:41

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Copyright © 2012 Present | Powered by AREWASOUND LTD.