Connect with us
Ramadan KAREEM

Labarai

Ganduje Ya Ba da Gudummawar Naira Miliyan 20 Ga Wadanda Gobara Ta Shafa A Kasuwar Katsina

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya ba da gudummawar naira miliyan 20 ga wadanda gobarar kasuwar Katsina ta shafa.

Ganduje ya ce za a yi amfani da kudaden ne don rage wahalhalun da wadanda abin ya shafa suka fuskanta.

Shi ma a ranar Talata ya gabatar da wasikar ta’aziya ga Gwamnan Jihar, Aminu Masari, yana yaba masa saboda kafa kwamiti mai karfi don gano ainihin musabbabin mummunan tashin hankalin.

Ya kara da cewa ko shakka babu abin takaici ne matuka ganin yadda lamarin bai shafi harkokin kasuwanci da jama’ar jihar Katsina ba kawai, har ma da mutanen arewacin kasar.

A nasa bangaren, gwamna Aminu Masari ya godewa gwamna Abdullahi Ganduje bisa wannan tallafi wanda ya yi imanin zai taimaka kwarai da gaske wajan taimakawa ‘yan kasuwar wajen gyara wani bangare na abin da suka rasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


CHECK OUT
[related_posts_by_tax]
How to Setup Glo Unlimited Browsing 2021

Airtel Bonus Code You Can’t Miss 2021

SOURCE: This post (Ganduje Ya Ba da Gudummawar Naira Miliyan 20 Ga Wadanda Gobara Ta Shafa A Kasuwar Katsina) firstly published at www.hutudole.com on 2021-04-07 11:03:51

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Copyright © 2012 Present | Powered by AREWASOUND LTD.