Smart News EverydayAREWASOUND
سُبحَانَ اللّهِ وَ بِحَمْدِهِ ، سُبحَانَ اللّهِ الْعَظِيمِ

La liga Gara na lashe kofin La Liga akan na lashe...

Gara na lashe kofin La Liga akan na lashe kyautar Pichichi sau takwas>>Messi

-

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

A ranar litinin Messi aka baiwa Lionel Messi kyautar Pichichi karo na bakwai wanda hakan yasa yanzu ya wuce Telmo Zarra ya zamo dan wasan da yafi lashe kyautar a tarihi, amma duk da hakan dan wasa ya bayyana cewa yafi fifita lashe kofin La Liga akan kyautar.

Pichichi kyauta ce wadda aka baiwa dan wasan daya fi zira kwallaye masu yawa a  kowace kaka ta gasar La Liga, kuma Messi da Ronaldo sun dauki tsawon shekaru suna fafataea wurin lashe kyautar kafin Ronaldo ya koma Serie A shekara ta 2018.

Bayan Messi ya lashe kyautar, ya tattauna da Marca kuma ya bayyana masu cewa bai san ko zai lashe kyautar karo na 8 ba, sannan shi baya tunani akan hakan saboda kyautar bata dame shi ba, hasalima yafi fifita lashe kofin gasar La Liga akan kyautar Pichichi.

A karshe Messi ya kara da cewa Barcelona tana shan gwagwarmaya a wannan kakar, kuma basu cancanci barar da maki tsakanin su da Alaves da Getafe da kuma Real Madrid ba, amma zasu yi kokari cin wasanni masu yawa a jere domin su koma saman teburin gasar La Liga.

Read more at SOURCE: This post (Gara na lashe kofin La Liga akan na lashe kyautar Pichichi sau takwas>>Messi) firstly published at hutudole.com on 2020-12-22 20:35:17

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

Karanta Wannan:-  Court orders El-Zakzaky wife’s release for COVID-19 treatment –

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you

Karanta Wannan:-  Covid-19: An samu sabbin mutum 1,430 Da su ka kamu da cutar Coronavirus/covid-19 A Najeriya