Dandalin KimiyyaMuhimman Hanyoyi 5 Don tsare Na'urorin ku daga kutse

Muhimman Hanyoyi 5 Don tsare Na’urorin ku daga kutse

-

[related_posts_by_tax]

A duniyar zamani kuma a duniyar na’ura, babu wata na’ura mai ƙwaƙwalwa da za ta tsira daga kutse matuƙar tana kunne.

Muhimman Hanyoyi 5 Don tsare Na’urorin ku daga kutse

Duk wani rukuni na na’ura mai ƙwaƙwalwa kama daga na’urorin tafi-da-gidanka, ko na’urorin kasuwanci, ko na aikin ofishi, ko na sadarwa, ko wayoyin hannu, da dai sauransu ba za su tsira daga tarkon madatsa ba, domin idan mai kariya ya na da hanyoyi goma na kare kanshi, madatsi ya na da hanyoyi dari da zai iya yin kutse.

Sai dai duk da haka masana suka ce yawancin waɗanda ake yi wa datsa suna ba da ƙofa ne ko ƙarama ce.

Wasu lokutan kuma rashin ɗaukar matakan kariya, ko bayyana wasu sirruka na na’ura kan iya sa a musu datsa ba tare da saninsu ba, ya dai danganta ga wane irin datsa aka shirya musu da yadda za a samu nasara a kansu.

Amma a lamarin manyan wayoyin zamani irinsu Android, mafi yawan hanyoyin da za a samu nasara a kan masu su shi ne ta hanyar ba su ƙofa, don a wannan zamanin an gano mafi yawan masu riƙe wayoyin ba su san abunda zai cutar da wayoyinsu da wanda ba zai cutar ba.

A wannan rubutun za mu ga waɗanne hanyoyi ne ya kamata a bi don kare kai daga madatsa.

Yin kutse wa wayar Android kan iya zama da manufofi da dama, kamar yi don:

  • ƙeta
  • tallace-tallace
  • neman kuɗin fansa
  • leƙen asiri
  • rusa wani lamari ko kuma wayar gaba ɗaya

Da sauransu, ya dai danganta ga don wace manufa ne aka yi kutsen. Sannan wasu lokutan su kan iya yin kutsen cikin na’urar mutum kuma su gama abunda za su yi ba tare da saninshi ba.

Amma kowanne daga cikin jerin nan ya kasance mai matuƙar hatsari ne, don haka ya kamata a ɗauki wasu matakai da zai hana yin kutse cikin wayoyi.

Karanta jirin Hanyoyin a shafin Flowdiary {shafin fasahar zamani a harshen hausa}

Sanin wadanan hanyoyi yana da muhimmanci sosai do kare na”urorin ku da ku kanku.

Muhimman Hanyoyi 5 Don Kare Wayar ‘Android’ Daga Annobar Na’ura Da Kutse >>

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you