LabaraiHotuna: An ceto wata yarinya da iyayenta suka kulle...

Hotuna: An ceto wata yarinya da iyayenta suka kulle tsawon shekaru 10 a Kano.

-

An ceto yarinya ƴar shekara 15 da iyayenta suka ɗaure tsawon shekara 10 a jihar Kano da ke arewa mao yammacin Najeriya.

Rundunar ƴan sandan jihar ne suka ceto yarinyar a ranar Litinin mai suna Aisha Jubril.

An kulle yarinyar ne a ɗaki tun tana ƴar shekara biyar.

Rundunar ƴan sandan Kano ta ce ta samu rahoto game da yarinyar misalin ƙarfe 11 na safe, kuma nan take Kwamishinan ƴan sandan jihar ya bayar da umarnin a gaggauta ceto yarinyar.

Kamar yadda BBCHAUSA na ruwaito.Ƴan sandan sun ce sun samu yarinyar cikin wani mawuyacin hali na tsananin yunwa da kuma buƙatar kula da lafiyarta saboda irin yanayin da suka samu wurin da aka kulleta, ku duba hotunan anan Continue Reading>

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you