FadakarwaHotuna : Anyi Nasarar Daukar Hoton Ramin Zurmiya Na...

Hotuna : Anyi Nasarar Daukar Hoton Ramin Zurmiya Na Duniya (Black Hole)

-

Masu binciken sararin samaniya sunyi nasarar daukar hoton ramin zurmiya na black hole….
A karon farko, masana binciken sararin samaniya sunyi nasarar daukra hoton ramin zurmina na duniya, abinda ake kira black hole a turance. Shi da ramin black hole shine ginshikin duk duniyoyi da ake iya gani a sararin samaniya kamar yadda bincike ya nuna.
Masanan sunyi amfanin da na’urar Event Horizon Telescope (EHT), wadda ke amfani da jeri-jerin maduban hangen nesa, wato telescopes, da aka giggirka su a kusurwowi daban daban na duniya don leqen abubuwan dake wakana a sararin samaniya.

Hotuna : Anyi Nasarar Daukra Hoton Ramin Zurmina Na Duniya (Black Hole)

Hoton ramin, an dauke shi ne a ma’unin M87, wanda yazo daidai da tafiyar shekaru miliyan 55 a kirgar duniyar taurari.

“Wannan hoton da kake gani, yana nuna mana inda ba wani mahaluki da ya taba gani kafin yau” inji Dr Heino Falcke, wani jami’n biciken sararin samaniya na EHT, a lokacin ganawa da maneman labarai, yau a Brussels. Ya kara da cewa “Ni a ganina na, tamkar ace mun dan leko kofar wuta ne”.

HOTUNA 

Dan zobe-zoben dake kewaye da hoton wannan rami dai yazo daidai da hasashen da masanin kimiyyar makamashi, wato Albert Eeinstein ya yi don kwatanta karfin maganadison dake riqe da duniya, wato gravity.

Wannan hoto dai shine sheda mafi inganci dake tabbatar da samuwar ramin zurmiya na black hole da nau’rar Event Horizon ta hasko.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you