Labarai Hotunan bikin Dan gidan El'rufa'i gwamnan Kaduna

Hotunan bikin Dan gidan El’rufa’i gwamnan Kaduna

-

Advertisements
Advertisements


– An daura auren dan gwamnan jihar Kaduna, Bashir El-Rufai da amaryarsa Halima Nwakaego Kazaure

– Taron auren wanda ya gudana a Abuja a yau Asabar, 21 ga watan Nuwamba ya samu halartan manyan masu fada a ji

– Yan siyasa sun ajiye banbancin akida sannan suka dunga annashuwa da walwala a tsakaninsu

A yau Asabar, 21 ga watan Nuwamba ne aka daura auren dan gwamnan jihar Kaduna, Bashir El-Rufai da amaryarsa Halima Nwakaego Kazaure.

Taron auren wanda aka yi babbar birnin tarayya Abuja ya samu halartan manyan masu fada a ji, sarakunan gargajiya da attajirai.

Advert

A hotunan bikin da aka wallafa a shafukan sadarwa, an gano mahaifin ango, Gwamna Nasir Ahmed El-Rufai tare da matayensa cikin annashuwa da walwala.

Har ila yau an gano manyan mutane irin su tsohon sarkin Kano kuma aminin mahaifin ango, Muhammadu Sanusi II.

Daga cikin jami’an gwamnati da suka hallara akwai gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, tsohon gwamnan jihar Jigawa Mallam Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari, tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha.

Tsohon Shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, tsohon gwamnan jihar Niger, Dr Babangida Aliu, Shugaban jam’iyyar PDP ta kasa, Uche Secondus duk sun hallara.

Ga karin hotunan auren a kasa:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

You might also likeRELATED
Recommended to you