Rahotanni daga jihar Kano na cewa Hukumar Hisbah dake jihar ta gudanar da bincike daki-daki dan neman masu aikata ayyukan ashsha.
Rahoton wanda Sahara Reporters ta samar ya bayyana cewa Hisbah ta yi wannan bincike ne a jiya, Juma’a, 27 ga watan Nuwamba. Tace wani wajan Shakatawa me suna Hill and Valley dake Dawakin Kudu inda ma’aikatan wajan suka zagaya da hukumar dan ganin yanda lamura ke gudana.
Rahoton dai ya jawo cece-kuce sosai a shafukan sada zumunta.
Labarai masu alaka