Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta karyata rahotannin da ke cewa ta yi tyunkurin cafke dan gwagwarmayar Yarbawan, Sunday Igboho, a jihar Oyo ranar Juma’a 26 ga Fabrairu.
Jami’in hulda da jama’a na DSS, Dakta Peter Afunanya, ya karyata rahoton a cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin jum’a.
Hukumar tace wannan labarin kanzon kurege ne kuma tana Kira ga jama’a da su yi watsi da wannan labarin.