Connect with us
Ramadan KAREEM

Labarai

Jami’an Hukumar FRSC sun mayar wa da dangin wani fasinja da ya mutu a hatsarin mota N716,800 da suka tsinta

Published

on

Jami’an Hukumar FRSC sun mayar wa da dangin wani fasinja da ya mutu a hatsarin mota N716,800 da suka tsinta

Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta mayar wa da dangin fasinjan da ya mutu N716, 800 da aka samu a wani hatsari da ya faru a jihar Anambra.

Kwamandan sashin a Oraifite, Mista Bamidele Ayanwale, wanda ya mika kudin a ranar Talata, 6 ga Afrilu, ya ce an gano kudaden ne a lokacin da jami’an FRSC ke aikin ceto bayan hatsarin.

Ayanwale ya ce hatsarin wanda ya hada da motar Nissan mai lamba LSH-517YG da kuma wata babbar mota mai lamba GGU-83XA, ta faru ne a ranar 22 ga watan Maris, a Ozubulu da ke karamar hukumar Ekwusigo ta jihar Anambara.

Ya ce an mayar da kudin kudin na marigayiya Mrs Oparaocha, ga danta mai suna Mista Chibueze Oparaocha bayan an bayar da gamsasun hujjoji a rubuce.

A nasa bangaren, Chibueze Oparaocha, dan marigayin, ya gode wa FRSC bisa wannan karamci da gaskiya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


CHECK OUT
[related_posts_by_tax]
How to Setup Glo Unlimited Browsing 2021

Airtel Bonus Code You Can’t Miss 2021

SOURCE: This post (Jami’an Hukumar FRSC sun mayar wa da dangin wani fasinja da ya mutu a hatsarin mota N716,800 da suka tsinta) firstly published at www.hutudole.com on 2021-04-06 20:36:02

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Copyright © 2012 Present | Powered by AREWASOUND LTD.