Jam’iyyu 42 ne Basu Amince da sakamakon zaben kano ba :

Jam’iyyun siyasa arba’in da biyu a jihar Kano karkashin kungiyar jam’iyyar adawa CUPP sun nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaben gwamnan ranar Asabar, 23 ga watan Maris, 2019 da aka gudanar.
Sun yi zargin cewa an tafka magudi da rashin gaskiya a zaben.

Shugaban kungiyar CUPP na jihar, Mohammed Abdullahi-Rahi, ya bayyana matsayar kungiyar a wata da manema labarai a jihar Kano ranar Talata.

Ya yi zargin cewa zaben zagaye na biyu da hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta gudanar cike yake da magudi, rikice-rikice, yiwa jama’a barazana da hana mutane kada kuri’arsu.

KU KARANTA: Tofa – An kayyade kudin sadakin aure a kafatanin kasar nan.

Game da cewarsa, ta’ddanci da barazana ya faru a yawancin rumfunan zaben da akayi zabe ranar Asabar, inda akayi asarar rayuka, akayi siya-siyan kuri’u da wasu ayyukan da ya sabawa dokar zabe.

Yace: “Ya bayyana karara cewa irin rikice-rikicen da ya faru ranar ga watan Maris da ya kai ga soke zabubbukan wasu rumfunan zabe, bai kai yawan abinda ya faru ranar 23 ga watan Maris ba, amma duk da haka hukumar zabe tayi murus, ta sanar da sakamakon zaben.”

“Saboda haka, muna nuna rashin amincewarsu da sanar da Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin zababben gwamnan jihar da aka gudanar ranar 23 ga Maris.”

Leave a comment