FadakarawaJerin Muhimman abubuwa da ya kamata iyaye su sa...

Jerin Muhimman abubuwa da ya kamata iyaye su sa ni kafin su ba wa yara wayar salula ta zamani

-

Mutane da dama su na ganin ba wa yara wayar salula babbar illa ce a wannan zamanin, ya yin da wasu kuma su ke ganin yana da kyau a bawa yaro wayar ta salula, saboda kara wayar musu da kai a rayuwa irin ta wannan zamanin .

Shekaru da dama mutane su na ta faman maganganu akan iya shekarun da yaro ya kamata ya kai kafin a ba shi wayar salula ta zamani.

Wasu daga cikin dalilan da suka wo maganganun sun hada da amfani da wayar wurin kallon hotuna da bidiyon batsa, sannan takwai yiwuwar wayar za ta iya salwanta a hannun yaron, ko kuma fadawa tarkon ‘yan damfara na yanar gizo.

Gaskiyar magana dai ita ce, wayar salula ta na da matukar muhimmanci ga rayuwar al’umma musamman wurin sada zumuntaa.

Amma zancen dai-dai shekarun da ya kamata a ba wa yaro wayar salula, wannan ya danganta da yanayin yanda iyayen su ka dauki dan na su, saboda shekaru ba su ne abu mafi muhimmanci ba, hankali da tunani, da kuma irin yardar da iyaye su ka yi wa yaro ita ce abu mafi muhimmanci. Kuma su ne abubuwan da ya kamata iyayen sun fahimta kafin su ba shi waya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you