A baya da lokacin ajiye aikin Tsohon Shugaban ‘yansandan Najeriya, IGP Muhammad Adamu yayi a watan Fabrairu, Shugaba Buhari ya kara masa wa’adin watanni 3.
Saidai watanni 3 din basu cika ba, gashi Shugaba Buhari yayi nadin sabon Shugaban’yansandan.
An tambayi Ministan Harkokin ‘yansanda, Muhammad Dingyadi ko menene dalilin yin hakan?
Yace Shugaba Buhari ne ke da wuka da nama wajan nadawa ko sauke shugaban ‘yansandan dan haka idan yayi abinda doka ta bashi damar yi ba wani abu bane.