LabaraiKalli Zafafan Hotunan Jaruman Kannywood a yayin Murnar Zagayowar...

Kalli Zafafan Hotunan Jaruman Kannywood a yayin Murnar Zagayowar samun yanci

-

Ranar Samun’Yancin Kai..

Kamar yadda kowa yasani a yau ne Najeriya take murnar cika shekaru 61 da samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka na kasar Ingila.

Sai dai kuma wannan rana ta zo ne a wani irin yanayi, yayin da wasu suke yin murna, wasu kuma suna kokawa bisa matsanancin yanayin da suke ciki.

Idan mukayi duba da irin halin fargaba da tashin hankalin da al’umomin yankin Arewa maso yamma suke ciki, za mu gane cewa su a bangarensu babu wani ‘yanci da suka samu, domin kuwa tuni ‘yan ta’adda suka keace musu ‘yancinsu na yin rayuwa ba tare da fargaba ba, domin kuwa wasu an sace musu ‘yan’uwansu, wasu an kashe su an kuma kore su daga muhallansu, wasu an rabasu da gonakinsu da kasuwanninsu da duka dukiyoyin da suka mallaka.

A wani bangaren kuwa al’umma suke kokawa bisa halin matsin Tattalin Arziki da suke ciki a dalilin hauhawar farashi, wanda hakan yajawo mutane dayasa suke kwana da yunwa.

A wani bangaren kuma marasa lafiya ne suke ta kokawa bisa yajin aikin da likitoci masu neman ƙwarewa suka shafe tsawon lokaci suna yi, wanda hakan yasa marasa lafiya suke matukar galabaita.

To koma dai me yake faruwa, hakkin gwamnati ne ta inganta walwalar al’umma da jin dadinsu.

Me karatu a ganinka wane irin ‘yanci Najeriya tasamu acikin shekaru 61 da ta shafe a matsayin ‘yantacciyar ƙasa?

Daga Sabiu Danmudi Alkanawi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you