Connect with us
Ramadan KAREEM

Breaking News

Kano Pillars ta tafi hutu…

Published

on

Kungiyar Kano Pillars Fc ta Kano ta ba da hutun kwana hudu ga ‘yan wasanta da masu horarwa. Fagenwasanni.com

Mai magana da yawun kungiyar lurwanu Idris Malikawa ne ya bayyana hakan bayan ganawar da shugabannin kungiyar suka yi a ofishin shugaban kungiyar.

Lurwanu Idris Malikawa yace hutun ya fara ne daga ranar Laraba zuwa Lahadi 11/4/2021.

Kano Pillars ta tafi hutu...

Malikawa ya ce a lokacin hutun babu wani dan wasa da aka yarda ya yi balaguro a wajen Kano saboda dalilan hutun shi ne a ba su damar hutawa da yin shiri sosai gabanin rukuni na biyu na kakar da ke gudana.

Ya ce shugabannin sun yi godiya ga Allah Madaukakin Sarki, Gwamnati da mutanen jihar Kano saboda nasarar da kungiyar ta samu a farkon zangon kakar.

Hakanan an yabawa ‘yan wasa, ma’aikatan fasaha da masu horarwa, masu goyon baya, magoya baya da duk wadanda suka bayar da gudummawa ga ci gaban kungiyar, in ji Malikawa.

Ya ce shugabannin kungiyar da ma’aikatan kungiyar tare da masu horarwa suna aiki kafada da kafada don karfafa kungiyar da kwararrun ‘yan wasa a wasu sassan domin tabbatar da mafarkinsu a karshen kakar wasa ta bana.

Sai masu gida sun ƙare zagayen farko a matsayi na biyu a teburi da maki talatin da shida.


CHECK OUT
[related_posts_by_tax]
How to Setup Glo Unlimited Browsing 2021

Airtel Bonus Code You Can’t Miss 2021

SOURCE: This post (Kano Pillars ta tafi hutu…) firstly published at fagenwasanni.com on 2021-04-08 00:55:24

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Copyright © 2012 Present | Powered by AREWASOUND LTD.